Daga yammaci, Aljeriya.daga arewa maso yammaci, Tunis.
Libya kasar larabawa ce kuma tana daga cikin kungiyar tarayyar Afirika kuma tana daya daga yan kungiyan kasashen larabawa da kungiyar kasashen musulunci, har zuwa yau ita 'yar kungiyar kasashen Arewacin Nahiyar Afirka ce, kuma yar kungiyar kasashen da suke da man fetur ne.
Kasar Libya babbar kasa ce a wurin fadin Kasa amma sai dai mafi yawan kasar Sahara ce, Iyakar libya takai 1,759,540 km2 tanada babban iyaka da teku. Shugaban kasar daya shahara shine Muammar Gaddafi.
Libya da harshen misrawan da, wannan suna ya samu ne daga kabilar libo da suke zaune A jihohin da suke tsakanin Misra da Tunisiya.
dadin dadawa, akan kabilar libo kuma da akwai kabilu 'yan asalin Libya kaman Amazik da kabilar feneken. a karni na shida kafin haihuwar Annabi Isah daular kurtaja ta mamaye libya duk da karfinta Romawa sun kwace ta daga hannunsu, a karni na shida bayan haifuwar Annabi isah bizantinawa suka mamaye Libya. Kuma A karni na bakwai bayan haihuwar Annabi Isah sai larabawa suka shigo Libya
.
Libya ta samu ire-iren iko kamar haka:-
mulkin kafin tarihi.
lokacin fenekawa da Igregawa da rumawa
lokacin da Libya tana karkashin mulkin Amauiyawa da abbasiyawa a shekara ta 644
Mutunen Libya sun kai adadin 6000,000 a sahile a arewacin kasar kabilolin Libya su ne, larabawa, barbarawa, tubawa karaglawa ( hadin turkawa da larabawa ), Buzawa da 'yan tsurarun ( hausawa da bare-bari ).
harshen larabci shi ne harshen kasar, larabcinsu yana da bambanci da sauran na kasashen larabawa kuma da akwai harsuna da yawa masu bambancin harshen ( Amazik, Buzancitubanci da harshen Hausa ) shi ne harshen kasuwanci a birnin sabha da ke a kudancin kasar .
Addini
yawancin yan Libya musulmai ne (97%)
sauran adadin (3%) kawai kiristoci da yahudawa ne.
kuma Libya bata da shi'a samsam mabiya addinin yahudawa ( yahudawa ) yawancin su sun fita daga kasar bayan 1967 a yanzu saura 'yan tsirari a tirbule , Libya tana da 'yan tsirarun kyrke a tirbule da bangazi kuma suna da malamai kyrke daya yana Bangaze da zama
Jihohin Kasar
libya tanada jihohi talatin da biyu sune kamar haka:-