Maroko ko MorokoLarabci المغرب , (Al-Magrib) (ma'ana mafadar rana ko yamma). A yaren Abzinawa, kuma ⵍⵎⵖⵔⵉⴱFaransanciMoroc, cikaken sunan ƙasar shine Masarautar Maroko. da yaren Abzinanci ko kuma Berber ⵜⴰⴳⵍⴷⵉⵜ ⵏ ⵍⵎⵖⵔⵉⴱ da Larabci kuma المملكة المغربية Al-mamlaka al-magrabiyya Kasace dake, bin tsarin mulki salon sarauta dake Arewacin Afrika. Kasace ta asalin yan kabilar Abzinawa.ƙasar Maroko kasace dake da dogayen tsaunuka da kuma Sahara. Maroco ta yi iyaka da tekun Mediterranean daga Arewaci, sai koma tekun Atlantic da ga yamma, sai koma wajan kasa tayi iyaka da kasar Aljeriya da ga Gabas
Al'umar kasar Maroko yakai kimanin miliyan talatin da bokwai 37 million kuma tana da adadin fadin kasar kimanin da yakai kilomita 710,550 [1] (sukwaya mil 172 410). Babban birnin taraiya shine Rabat, kuma birni mafi girma shine Kasablanka. Sauran birane masu girma sun hada da Marrakeah, Tangier, Sale, Fea da kuma Meknes.
Hotuna
Assilah
Birnin Casablanca
Coat of Arms
Tutar kasar
Hamadan sahara cike da rakuma a cikin kasar Maroko
Kyawun sahara ada tsakar rana
Gida a bakin teku a kasar Maroko
Takalman gargajiya a kasar Maroko
Kasar Maroko a shekaran 1860
A'ada a kasar Maroko
Yaren Berber ko Abzinanci shine babban yare kuma mai asali a kasar kafin Larabci da ya shigo bayan mamayar da larabawa sukayi ma kasar. Musulunci ne babban addini na kasar.