Sallar Layya, Babbar Sallah, Eid al-Adha (larabci-ar|عيد الأضحى|ʿīd al-ʾaḍḥā|lit da turanci Feast of the Sacrifice), kuma ana kiranta da "Sallar Yanka/Sallar yin layya", shi ne biki na biyu da musulmai ke gudanarwa a duk duniya a kowace shekara, dayan bikin shi ne (Karamar Sallah), ana ganin wannan babbar ta fi daraja a cikin biyun. Allah ta'ala, ya karrama Annabi Ibrahim/Abraham (A.S), bayan ya mika wuya a Gare shi a kan yarda da yanka dansa Annabi Ismail (A.S) domin bin umurnin da Allah Ya bukace shi ya yi. Amma kafin Annabi Ibrahim ya yanka dansa, sai Allah ya aiko da babban rago ya yanka, sanadiyar haka ne ake yin yanka kuma ake raba naman gida uku, kaso daya, sadaka ga mabukata, na biyu a Raba wa 'yan'uwa, na uku wanda ya yi layyar ya ci abinsa.
A kalandar musulunci 'Islamic lunar calendar'.
Ana so a musulunce ka canja hanya a Yayinda kake dawowa daga idi, watau a canza hanya daga wadda aka bi a wurin zuwa.
Ranar Sallah
Sallar tana zuwa ne a kowane goma (10th) na watan Dhu al-Hijjah. A kuma kalandar duniya ta girigori ranar na canjawa a dukkanin shekara zuwa shekara, ta hanyar rage kwanaki goma sha daya (11) daga ta Hijira.
Babbar sallah Rana ce mai dimbin tarihi a duniyar musulunci da misulmai wadda take zuwa bayan an yi sallah karama da wata 2 da kwanaki 20. Ranar babbar sallah rana ce wadda dimbin miliyoyin musulmin ke fitowa su je filin idi domin su hallarci sallar nafila raka'a biyu domin nuna godiya ga mahaliccinsu da nuna murnarsu a gare shi da ya ba su damar halattar wannan rana a tarihin rayuwarsu, a wannan ranar ana yanka abun layya abun da ya sawwaqa ga mutum daga rago, tunkiya, bunsuru, akuya, sa, shanu, shanuwa, rakumi amale, rakuma. Wadannan sune jinsin dabbobin wadanda ake layya dasu kuma rogo ya fi kowane daraja haka rakuma tafi kowannen su karancin daraja wato itace mai daraja ta can kasar. Akanko mutum ya yanka abun layyar sa ya Ciro wasu sassa acikindabba</nowiki>r yafi kamar yadda sunnar manzon Allah (s.a.w) ta nuna. Yin layyar bin sunnar baban annabawane wato Annabi Ibrahim (a.s) kuma bin KO cika umarnin Allah be inda yake cewa " kayi sallah ga ubangijinka kuma kayi sukar rakumi (wato layyar).
Ba'a siyarda manan layya haramunne wanda ya siyar yayi laifi agun Allah, domin Anaso awadatar DA kowa
Ba anyi layya sai a rarraba wa mafi kusanci daman layyar musamman makwafta DA makusanta, domin wanda bayadashi yasamu domin ba'abakin cikin awannanan ranar Anaso kowa yaiyita nishidi DA wallala.
A ranar babbar sallah akanje ziyara ta musamman ga makusanta DA makwafta domin tayasu murnar wannan Rana me matuqar girman daraja kamar yadda ake aiwatar a ranar karamar sallah. Wannan yawon yafi kebantuwa ga YARA DA wasu daga iyayen YARA musamman sabbin aure zuwa gidajen iyayensu domin tayasu murnar wannan Rana, haka amatayinka na wanda aka ziyarta yanada matukar kyau kabada barka da sallah (wato wani Dan ihsani na kidi, nama, cincin, dabino, ds-ds). Bayan ka zuba abinci sunci sunkoshi sai ayimusu wannan ihsani.
Gudanar da bikin sallah babba ya banbanta kowacce kasar DA kuma kowacce al'adar DA yadda take aiwata danata bikin sallah baba DA karama, ya danganta DA yanayin al'adarsu.
[1]