Jihar Osun jiha ce dake kasar Najeriya.Tana da yawan fili kimanin kilomita araba’in 9,251 da yawan jama’a kimani miliyan hudu da dubu dari daya da talatin da bakwai da dari shida da ashirin da bakwai (jimillar shekarar dubu biyu da biyar 2005). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Osogbo. Rauf Aregbesola, shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta dubu biyu da sha daya 2011 har zuwa yau ya sauka ya mika wa Adegboyega Oyetola.bayan ya samu nasarar cin zaben da aka gudanar. Mataimakiyar gwamnan ita ce Grace Titilayo Laoye-Tomori. Dattijan jihar su ne: Ademola Adeleke, Christopher Omoworare Babajide da Olusola Adeyeye.
[1]
Jihar Osun tana da iyaka da jihohin hudu: Ekiti, Kwara, Ogun kuma da Ondo.