Muhammad Bima Enagi
Muhammad Bima Enagi (an haife shi a ranar 7 ga watan Satumba, shekarar 1959) ɗan siyasa ne Nijeriya, kuma sanata mai wakiltar gundumar Sanatan Neja ta Kudu ta Jihar Neja a Majalisar Dokokin Najeriya ta 9.[1][2][3][4] IlimiMuhammad Bima Enagi ya samu digiri a fannin binciken yawa a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya a shekarar 1982.[5] Ƙwarewar sana'aYa fara aikin sa a hukumar Quantity Surveying tare da Owah Unik Consultants, Warri. Daga baya kuma ya shiga aikin gwamnati inda yayi ritaya a matsayin Darakta a Babban Bankin Najeriya.[6][5] Harkokin SiyasaSunan Sani Mohammed ya maye gurbin ɗan takarar sanatan Neja ta kudu sannan Enagi an zaɓe shi a zaɓen ranar 23 ga watan Fabrairu, shekarar 2019 na yankin Sanatan Neja ta Kudu inda ya samu ƙuri'u’u 160,614 yayin da dan takarar Jam’iyyar Democratic Party Shehu Baba Agaie ya samu kuri’u 90,978.[7][3] Duba kuma
Manazarta
|