Sani Mohammed dan siyasan Najeriya ne kuma tsohon dan majalisar dattawan Najeriya a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress .
An haifi Mohammed a garin Bida, jihar Neja . Ya taba zama sanata na Yankin Sanatan Neja ta Kudu a shekara ta (2015–2019)..[1][2]
Ya zo na uku a takarar sanata a babban zaben shekara ta 2019. Kwamitin Ayyuka na kasa na jam'iyyarsa ne suka wanke shi tare da sauran sanatocin shiyya, a ranar 4 ga watan Oktoban shekara ta 2018 don fafatawa a zaben fidda gwani. Daga baya, an sauya sunansa a minti na ƙarshe don Bima Mohammed Enagi.
Kyaututtuka da Girmamawa
- Doctor of Science (Honoris Causa): Jami'ar Gregory, Uturu, Najeriya.
Manazarta
- ↑ "Sen. Sani Mustapha Mohammed". National Assembly | Federal Republic of Nigeria. 2018-03-11. Archived from the original on 2018-03-11. Retrieved 2019-09-27.
- ↑ "After Shehu Sani another senator dumps APC" [permanent dead link], Sahara Reporters, 2019 [dead link]