Rukunnan Musulunci Biyar (arkān al-Islām, larabci أركان الإسلام; ko arkān al-dīn, larabci أركان الدين, Rukunnan addini, Shika-shikan addini) abubuwa ne ko ayyuka waɗanda ginshikai ne, guda biyar a Musulunci, wadanda wajibai ne akan kowane mai imani, kuma sune farkon ginshikin rayuwar Musulmi. Suna nan tattare a shahararren hadisin nan na mala'ika Jibril.[1][2][3][4]
Shahada ita ce miƙa wuya da tabbatar da Imani da bada gaskiya dake yarda da cewar babu wani abun bauta idan ba (Allah) ba, kuma Annabi Muhammad Manzon Sa ne, Kalman shahada dai rukuni ne na farko daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar, wanda wajibi ne sosai mutum ya kiyaye ta , tana shigar da mutum cikin Musulunci in har ya furta , kuma ya kudur ce a zuciyar shi ,kuma yayi aiki da ma`anan abinda ya firta, kuma tana fitar da Mutum daga Musulunci idan ya saɓa ma`anar kalman ta hanyan yin saɓo ko shirka ko ya aikata wani aiki dake fitar da mutum daga Musulunci
Ma`anarta shine ka yarda akan karan kanka ba tilasta ka akayi ba cewa Allah shi kaɗai zaka bautamawa , shine ka tsayar da Tauhidi guda uku Rububiyya da Uluhiyya da Asma`i wassifat , kuma baza ka haɗa shi da kowa ba a gurin bauta , wato baza kayi Shirka ba ko Tsafi ko wani nauyin na hakan, kuma kaji ka yarda cewa AnnabiMuhammad manzan Allah. Ma`ana ɗan aike ne daga Allah. Ma`ana duk abinda AnnabiMuhammad yace zaka yarda kuma ka gasgata ,abinda yayi umurni dashi kuma ko yayi hani, zaka aika ta sau da kafa.
.[9] Jawabi ne da yake a tsare, kuma ana furta shi ne da Larabci: lā ʾilāha ʾillā-llāhu muḥammadun rasūlu-llāh, (لَا إِلٰهَ إِلَّا الله مُحَمَّدٌ رَسُولُ الله) "Babu abun bautawa da gaskiya sai Allah (kuma) Annabi Muhammad Manzon Allah ne. Furta wannan jawabin nada muhimmanci sosai, Kafin mutum yazama Musulmi, ko ya dawo musulunci.[10]
Salah: (Sallah)
Sallah (ṣalāh) itace bautar musulmai, Sallah ta kunshi yin salloli biyar kamar yadda Sunnah tazo dasu; sunayensu akan lokutan Amfani: Fajr (Subhi), Dhuhr (rana), ʿAṣr (Yamma), Maghrib (Almuru), da kuma ʿIshāʾ (dare). Sallar Fajr ana gudanar da ita ne kafin fitowar(tasowar) rana, Dhuhr kuma ana yinta ne a tsakiyar rana, bayan rana yayi zawali, Asr kuma da yammaci ake yinta kafin faduwar rana, Maghrib da almuru bayan rana ya fadi, sannan sai sallar Isha'i da akeyinta acikin dare. Duk wadannan salloli anayinsu ne ta hanyar kallon Kaaba a Mecca daya samar da muhimmin ginshiki a cikin alumman Musulmi. Musulmi sai sun wake jiki kafin yin Sallah; wannan wankin ake kira da wudu
Zakāh: (Zakkah)
Zakkāh Zakka rukuni ne daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar ana bayar da wani sashi ne na dukiyar mutum idan dukiyar ta kai nisabi.
Hajj itace ziyarar ibada dake faruwa a kowace watan musulunci na Dhu al-Hijjah zuwa Makkah. Kowani musulmi baligi dake da iko ya zama wajibi yayi aikin hajji a rayuwarsa koda sau ɗaya ne,
Hajji rukuni ne daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar ga wanda Allah ya bashi ikon zuwa ,ana yin aikin hajji ne kaɗai a makkah, kuma ba`a son mutum ya tafi aikin hajji alhali akwai bashi akan shi ko iyalansa na cikin wani hali ,ko kuma zasu shiga idan har ya tafi.
.[14]