Ahmadiyya (Urdu احمدیہAhmadiyya) tafiyar imani ce ta addini wadda aka kafa ta a ƙarni na (19), Mirza Ghulam Ahmad ne wanda mabiyan sa suka haƙiƙance kan cewar shine Mahdi ya kafa tafiyar. An kafa tafiyar ne tun kafin Indiya ta rabu zuwa wannan Indiyar ta yanzu wato rabewar ta da Pakistan da Bangladesh.
Ahmad yaso ya sabunta Musulunci, tare da da'awar dawo da ainahin koyarwa ta addinin Musulunci.a shekara ta alif( 1914), tafiyar ta rabe zuwa gida biyu, a sakamakon wanda zai zamo magajin Ahmad kuma har yanzu waɗannan ɓangarorin sunanan.
Mirza Ghulam Ahmad yayi da'awar cewa ya cika annabatar Mahdi. Ana yi masa laƙani da Mujaddadi na ƙarni na( 14), kuma Yesun da aka alkawarta zuwan sa.[1][2][3][4][5]
Yan Ahmadiyya na ɗaukar kansu a matsayin Musulmai kuma suna da'awar sunayin addinin Musulunci ne wanda Annabi Muhammad ya koyar.
Mirza Ghulam Ahmad ya kafa tafiyar ne a shekara ta alif(1889 ), kuma ya saka mata suna Ahmadiyya Muslim Jamaat Fatan sa shine ya dawo da ruhin Musulunci. .
Ainahin tafiyar Ahmadiyya ya tsage zuwa gidaje biyu[6] bayan rasuwar Nooruddin,magajin Ghulam Ahmad na farko.
Waɗannan tafiyoyin biyu sune Jama'ar Ahmadiyya da kuma Jama'ar Ahmadiyya ta Lahore (Ahmadiyya Anjuman Ishaat-i-Islam, AAIIL). Ɓangarorin nada bambanci ga hanyar koyarwa a tsakanin su.[6][7]
Babban ɓangare na Jama'ar Ahmadiyya na da rassa a sama da ƙasashen duniya (190), babbar cibiyarta na a birnin Landan na Ingila.
Karamin tsagin kuma da akafi sani da Jama'ar Ahmadiyya na Lahore nada cibiya a Lahore, kuma anfi sanin su a Jamani, Autraliya da Pakistan.
Abinda ke kawo rigima shine fahimtar Ahmadiyya dangane da rasuwa da dawowar Annabi Isah da kuma mahangar su ga Jihadi.
Hakanan ma Yan Ahmadiyya Nada bambancin ta Ƙur'ani( 33:40. ), Wannan aya tana magana akan cewa Annabi Muhammad shine cikamakon Annabawa. Sai dai mabiya Jama'ar Ahmadiyya ta Lahore basu da taraddadi dangane da wannan batun domin su basu kallon Mirza Ghulam Ahmad matsayin Annabi. A wannan dalilin ne yasa sukafi kusanci da aƙidar Musulunci.
Yan Ahmadiyya sun fassara ƙur'ani da dukkannin manyan harsunan duniya. Kuma suna yada aƙidun su da da'awar su awa (24), a tashoshin su na talabijin din su waɗanda suka haɗa da, MTA 1,MTA 2, MTA 3 (domin Larabawa masu kallo) kuma kwanannan suka ƙaddamar da sabuwar tashar MTA Africa. Yan Ahmadiyya na samar da malamai, likituci,masu kare yancin Dan Adam a ƙasashen da suka cigaba.
Zarge-Zarge
Musulmai mabiya Sunnah na kallon yan Ahmadiyya da masu aikata Bidi'a saboda imanin da sukayi cewa Ahmad Ghulam Annabi ne kuma shine Mahdi kuma Annabi Isah da zai dawo kuma basu yadda da ce Annabi Muhammad ne Annabin ƙarshe ba.[8][9]
Dangane da yadda yaso ya Annabtar da kansa kuwa yace shine Annabi Isah kuma yadawo ne domin ya karya Gicciye.[10] Mafi rinjayen musulmai basu danganta Yan Ahmadiyya da wannan sunan, sunadai kallon su ne a matsayin wasu masu wani sabon Addini wanda wani ya samar. Ba kamar Musulunci ba wanda shi Annabi Muhammad ne yazo dashi amma bashine ya samar da shiba.[11].
Akida
Acikin aƙida da abubuwan da Yan Ahmadiyya sukayi imani dashi akwai shiƙa-shiƙan Musulunci guda biyar (wato, Shahada, Sallah, Azumi, Zakka, Hajji) kuma suke yinsu, sannan kuma sunyi imani da shiƙa-shiƙan imani guda shida kamar dai yadda Musulmai Mabiya Sunnah sukayi. Hakanan kuma sun yadda da Al ƙur’ani kuma suna kallon Ka'aba matsayin Alkibla lokacin da zasuyi Sallah, kuma suna bin Sunnah da Hadisi.[12][13][14][15][16]
Alkalumma
Yazuwa shekarar 2016,an ƙiyasta adadin ƙasashe( 209) ne a duniya inda za'a iya samun yan Ahmadiyya. Babu ƙasar da Ahmadiyya ke da rinjaye.[17] A wasu ƙasashen kamar Pakistan an haramta Ahmadiyya gabatar daya.[18] Gabaɗaya wannan dalilinne yasa yakasance abu mai wahala ga Ahmadiyya ta kafa wasu ƙungiyoyinta masu zaman Kansu. Sakamakon haka Yan Ahmadiyya na ikirarin sunkai gwamman miliyoyi;[19] bugu da ƙari wasu majiyoyi masu zaman kansu sun ruwaito cewar akwai ƙididdigar adadin jama'ar Ahmadiyya sunkai miliyan( 10 zuwa 20),[20] gaba dayan duniya anyi ƙiyasin yan Ahmadiyya sunkai adadin kaso( 1% ),na al'umar Musulmai.[21] a shekara ta (2001), wata Insakulofidiya mai suna Christian Encyclopedia ta wallafa cewar Tafiyar Ahmadiyya tafi kowacce darika a Musulunci saurin yaɗuwa.[22] Ta kuma ƙiyasta cewa ƙasar da tafi kowacce yawan yan Ahmadiyya itace Pakistan, da ƙiyasin (4%), na al'umar ƙasar. Sai kuma Jama'ar Ahmadiyya ta Lahore mai mabiya( 0.2% ), a ƙasar ta Pakistan.[23] An ƙiyasta cewa yan Ahmadiyya ka iya kaiwa (60,000 zuwa miliyan 1 a Indiya).[24].
Breach of Faith. Human Rights Watch. June 2005. p. 8. Retrieved 29 March 2014. Estimates of around 20 million would be appropriate
Larry DeVries; Don Baker; Dan Overmyer. Asian Religions in British Columbia. University of Columbia Press. ISBN978-0-7748-1662-5. Retrieved 29 March 2014. The community currently numbers around 15 million spread around the world
Juan Eduardo Campo. Encyclopedia of Islam. p. 24. ISBN0-8160-5454-1. Retrieved 29 March 2014. The total size of the Ahmadiyya community in 2001 was estimated to be more than 10 million
↑A figure of 10 to 20 million represents 0.62% to 1.25% of the worlds Muslim population.
↑As of 2001[update] the Ahmadiyya Movement had been the fastest growing sect according to the World Christian Encyclopedia for a number of decades. For this, see earlier editions. The 2001 edition placed the growth rate at 3.25%, which was the highest of all Islamic sects and schools of thought. See:
David B. Barrett; George Thomas Kurian; Todd M. Johnson, eds. (15 February 2001). World Christian Encyclopedia. Oxford University Press USA. ISBN0195079639.
↑The Lahore Ahmadiyya Movement has unofficially stated its total population to be up to 30,000, of which 5,000 to 10,000 live in Pakistan. On this basis, the Lahore Ahmadiyya Movement represents approximately 0.2% of the total Ahmadiyya population.See: