Ibrahim Yakubu El-Zakzaky (An haife shi a ranar 5 ga watan mayun shekarata alif dubu daya da dari Tara da hansin da uku miladiyya 1953) malamin addinin musulunci ne, kuma shugaba a bangaren mabiya mazhabar Shi'a kuma Dan gwagwarmayar Addinin musulunci a Najeriya. Shi ne ya kafa ƙungiyar 'yan' uwa musulmi ko kuma ace muslim brothers a shekara ta alif 1979 a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, mutanen gari kuma na ce masu 'yan Shi'a ko 'yan Burazas. Zakzaky yasha tuhuma da dauri da dama saboda Gwagwarmayar sa da yakeyi akan rashin adalci tare da cin hanci da rashawa da kasar sa ke fuskanta daga mahukuntanta. A tsarin gwagwarmayarsa ya dage akan cewa lallai Addinin musulunci ne kadai zai kawo mafita ga rikitattun matsalolin zamantakewa da siyasa, wadanda a tsawon shekaru suke maida cigaban kasar baya.[1][2] A wata lakca da ya gabatar na tunawa da Makon Sheikh Uthman Bn Fodio (a watan Mayu shekarata alif 2023) da kungiyar Dalibai wato Academic Forum of Islamic Forum ta shirya, Zakzaky ya bayyana cewa yana ci gaba da Jihadin Uthman Bn Fodio domin ganin Musulunci ya zama mai Hukunci. wannan fata nasa ba'a Najeriya kadai ya tsaya ba, har ma da kasashen yammacin Afirka baki daya. A wata lacca da ya gabatar a daidai wannan lokaci a garin Sokoko (a ranar 20 ga watan Mayu, shekarata alif 2023), daya daga cikin masu goyon bayansa, Dokta Nasir Hashim ya bayyana cewa, ba wai gadar zalunci da cin zali da mulkin mallaka ba ne, amma burin Zakzaky shi ne kawai fata ga Afirka baki daya.
Tarihin Ibrahim Zakzaky
Haihuwar Ibrahim Al'Zakzaky
An haifi Sheikh Ibrahim Al'zakzaky a garin Zariya na jihar KadunaNajeriya a ranar 5 ga watan Mayu, shekara ta alif da ɗari tara da hamsin da you (1953), dai-dai da (15 Sha'aban 1372 AH). Ya halarci makarantar Allo sannan sai ya wuce makarantar Larabci a shekara ta alif (1969-1970), Sannan ya yi makarantar larabci ta SAS a garin Kano daga alif 1971-1976,miladiyya inda ya samu iliminsa na grade II. Sai kuma jami'ar Ahmadu Bello (ABU) a garin Zariya (1976-1979), inda ya kammala karatun digirinsa a kan fannin ilimin sanin tattalin arziki (Economics) inda ya samu kyakkyawan sakamako saboda ya kasance dalibi mai hazakar gaske. A lokacin karatunsa na jami'a ne Malamin ya zama shugaban kungiyar dalibai Musulmai ta kasa wato (MSSN). Daga bisani kuma ya zama mataimakin shugaban babbar kungiyar ta kasa mai kula da kasashen waje a shekarar 1979.
Daga nan ne kuma Sheikh Ibrahim Zakzaky ya fara nuna goyon bayansa ga juyin juya halin da aka yi a kasar Iran a shekarar 1979 miladiyya Daga nan kuma sai Zakzaky ya tafi kasar ta Iran. Bayan dawowarsa daga Iran ne ya cigaba da yada Gwagwarmayar dawo ma addini a kasar har zuwa shekarun 1990 inda ya tara mabiya masu dimbin yawa akasari matasa ne masu kaunar addini.
Kungiyar 'Yan'uwa Musulmi
Ibrahim Al'Zakzaky ya kafa kungiyar da ake kira 'Islamic Movement in Nigeria' wadda ada ake kira da 'Muslim brothers' ko kuma 'yan'uwa musulmi a Hausance.
Rikice-rikicen Kungiyar Yan'uwa Musulmi
Wannan kungiya ta El-zakzaky ta sha fama da rikice-rikice da rigingimu tun daga farkon kafata har zuwa yanzu. Fitattu daga cikin rikicin da kungiyar ta fuskanta sun haɗa da wanda ya faru a shekarar 1998 da kuma na shekarar 2014 da na 2015.
Rikicin Yan shi'a na 2014 a Zariya
A ranar 25 ga watan Yuli na shekarar 2014 ne aka samu tashin hankali tsakanin yaƙungiyar r 'yan uwa musulmi mabiya zakzaky da sojojin Najeriya a birnin Zariya, a yayin gudanar da lumanar zanga zanga akan nuna goyon bayan mutanen falasdinu inda mutane 35 suka rasa rayukansu ciki har da 'ya'yan Ibrahim Zakzaky guda uku (3). 'Ya'yan shugaban ƙungiyar da aka kashe, biyu daga cikinsu ɗaliban injiniyarin ne a wata jami'a dake china, dayan kuma dalibi ne a jami'atu Mustapha dake Lebanon. Rikicin da kungiyoyin kare hakkin bil Adama na duniya da dama ciki har da babbar kungiyar kare hakkin bil Adama ta duniya.
Rikicin kungiyar 'yan'uwa musulmi na 2015
Haka ma a birnin na Zariya ne a shekarar 2015 sakamakon 'ya kungiyar 'yan'uwa musulmi mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky sun tare hanyar da babban Hafsan Sojojin kasar na wannan lokacin, wato Tukur Yusuf Buratai zai wuce a lokacin wata ziyara da ya kai birnin na Zariya. Sai sojojin suka bude wuta a kan 'yan Shi'an, wadanda suka tare hanyar. Lamarin da ya yi muni sosai inda har ya kai ga rushe muhallan ibadarsu da ma makabartar mabiya Shi'a din. Sannan daruruwan mabiya kungiyar sun rasa rayukan su. Haka nan dai lamarin ya yi sanadiyyar rasa rayukan na hannun daman Shaikh Zakzaky wato Sheikh Muhammad Mahmud Turi da wasu daga cikin 'ya'yan jagoran wato Ibrahimu Zakzaky. Shi ma da kansa Zakzaky da mai dakinsa Zinatu sun samu munanan raunuka a lokacin tashin hankalin inda daga bisani jami'an tsaro sukayi awon gaba da su aka kai su gidan gyara halin hukumar kasar ta Najeriya na tsare da su har zuwa shekarar 2021 sannan aka sallamesu. Saidai kuma 'ya'yan kungiyar ta 'yan'uwa musulmi sun yi ta gwagwarmaya da yin zanga-zanga a wasu daga biranen kasar domin ganin an sakar masu jagoran nasu. Wanda dai lamarin na zanga-zangar ya haddasa wadansu tashe tashen hankulan inda har aka samu rashin rayuka da dama.
Amma sakamakon zaman wata kotu a kasar wanda ta yi a ranar 2 ga Disambar 2016, ta yanke hukuncin umartar hukumar Najeriya da ta gaggauta sakin Sheikh Zakzaky da matarsa tare da biyansa diyyar naira miliyar 50, tare da wadansu kudirorin.
A watan Janairu na 2018 ne aka soma jin duriyar malam Ibrahim zakzaky, inda ya gabatar da wani takaitaccen jawabi wanda ba a san ko wanne waje ba ne.
Rayuwar Zakzaky ta kashin kai
Shaikh Alzakzaky ya auri matarsa Zeenah Ibrahim zakzaky, suna da 'ya'ya tara tare da shi. Yanzu 'ya'yansu uku suka rage namiji daya da mata biyu. Uku daga 'ya'yan Zakzaky an kashe su ne Zariya, a lokacin zanga-zangar lumana ta nuna goyon Falasdinu, su ne Ahmad Ibrahim Zakzaky, Hamid Ibrahim Zakzaky da kuma Mahmoud Ibrahim Zakzaky, kuma hakan ya faru ne a 2014, a karkashin Gwamnatin Goodluck Ebele. Har ila yau, an kara kashe wasu yayansa maza ukku a ranar 12 ga watan Disamban 2015, wanda suka haka da Ali Haidar Ibrahim Zakzaky, Humaid Ibrahim Zakzaky da kuma Hammad Ibrahim Zakzaky. Kuma hakan ya faru ne a karkashin Gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
↑Dan Issacs (1 October 2001). "Nigeria's firebrand Muslim leader". BBC News. Archived from the original on 26 January 2020. Retrieved 28 February 2014.
↑ Connor Gaffey (16 December 2015). "Who is Sheikh Zakzaky, Nigeria's Most Powerful Shiite Muslim?". Newsweek Magazine. Archived from the original on 8 September 2021. Retrieved 12 April 2016.