Bagdaza
![]() ![]() Birnin Bagdaza ko Baghdad (lafazi ˈ|bæg|dæd|,_|bəg|ˈ|dæd; larabci|بغداد |bagh|ˈ|daad) Shi ne babban birnin kasar Iraq. Adadin yawan al'umman Baghdad, sun kai kusan miliyan takwas da dubu Dari bakwai da sittin da biyar (8,765,000), [note 1] haka yasa ya zama gari mafi yawan al'umma a ƙasar Iraq, kuma birni na biyu a yawan Mutane a ƙasashen Larabawa (bayan Birnin alkahira, Egypt), kuma birni na biyu a Yammacin Asiya (bayan Tehran, Iran). Yana nan ne a kusa da Tigris River, an samarda da birnin ne tun daga karni na 8th kuma tazama babban birnin Daular Abbasiya. A Dan kankanin lokaci bayan kafa birnin, Baghdad tazama wani muhimmin cibiyar al'adu, kasuwanci, da kuma zama cibiyar ilimi a tsakanin Kasashen Musulmi. Haka, da Karin samarda manya manyan shahararrun makarantun kamar (misali., Gidan Hikima), yasa birnin tasamu suna na zama "Cibiyar koyon Ilimi". Baghdad takasance babban birni a Middle Ages na yawancin lokutan zamanin Abbasiya, da yawan al'umma dasuka kai kimanin sama da miliyan a waccan lokaci.[4] Birnin yakasance babban tarwatsewa a hannun Mongol Empire a 1258, wanda ya haifar da faduwa da raguwa acikin zamunai da dama. Bayan samun yancin Iraq (bayan kasancewarta British Mandate of Mesopotamia) a 1938, Baghdad tasake farfadowa a matsayin ta na cibiyar Al'adun Larabawa. A wannan zamanin Birnin Bagdaza ta fuskanci tasgaro da lalace lalacen gine-gine da kone-kone, saboda 2003 invasion of Iraq, da yakunan da suka rika biyo baya Yakin Iraq wanda yakaiga har zuwa watan December 2011. A wadannan shekaru, Birnin yatasamun farmaki daga insurgency. Yakin yahaifar da lalacewar substantial loss of cultural heritage and historical artifacts kamar su. A shekara ta 2012, ansanya Baghdad acikin mafi rashin kyawun wurin zama da mutum zai rayu aciki a duniya,[5] kuma ansanya ta daga Mercer a matsayin mafi lalacew na 221 na manyan birane akan ingancin rayuwa.[6] Hotuna
Manazarta
|