Muhammad Shamsul Huq
Muhammad Shamsul Huq (12 ga watan Oktoba shekara ta 1912 zuwa 23 ga watan Fabrairu shekara ta alif dubu biyu da shidda 2006) ɗan siyasan kasar Bangladesh ne kuma malami. Ya yi aiki a matsayin ministan ilimi a tsohuwar Gabashin kasar Pakistan, kuma ya zama Ministan harkokin waje shekaru shida bayan samun 'yancin a kasar Bangladesh. [1] Shamsul Huq ya kuma yi aiki a matsayin mataimakin shugaban jami'a a Jami'ar Dhaka da Jami'ar Rajshahi . Gwamnatin kasar Bangladesh ta ba shi lambar yabo ta Ekushey Padak a shekara ta alif dubu biyu da ukku 2003. [2] Rayuwa ta farko da ilimiAn haifi Shamsul Huq a ranar 12 ga watan Oktoba shekara ta 1912 ga iyayen Musulmi na Bengali Karimul Huq da Mahmuda Khatun a ƙauyen Pashchimgaon a Laksam, Gundumar Tipperah, Lardin Bengal . A shekara ta 1927, ya wuce jarrabawar karatun sa daga makarantar sakandare ta Faizunnisa-Badrunnisa da ke Paschimgaon . Ya kammala karatun Intermediate of Arts daga Kwalejin Feni a shekara ta 1929. Shamsul Huq ya sami digiri na farko a fannin tattalin arziki da falsafar siyasa daga Kwalejin Islama ta Calcutta a shekara ta 1931. Ya sami digiri na biyu daga Jami'ar Calcutta a 1933. Ya kuma sami horo daga Jami'ar London a shekara ta 1945 zuwa shekara ta 1946, a karkashin Shirin Gyaran Ilimi na Bayan Yaƙi . AyyukaHuq ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban Jami'ar Rajshahi na uku daga 31 ga watan Agusta shekara ta 1965 zuwa 4 ga watan Agustan shekara ta 1969. [3] Daga nan ya yi aiki a Gwamnatin kasar Pakistan a karkashin Janar Yahya Khan a matsayin minista a Ma'aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha har zuwa samun 'yancin kasar Bangladesh. Daga 23 ga watan Satumba shekara ta 1975 zuwa 1 ga watan Fabrairu shekara ta 1976, Huq ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban Jami'ar Dhaka na goma sha biyar. [4] Ya zama Ministan Harkokin Waje na biyar a kasar Bangladesh a watan Nuwamba 1975, yana aiki da wannan matsayi har zuwa Maris shekara 1982. Daga 1977 zuwa 1978, Shamsul Huq ya kasance memba na kwamitin ba da shawara na shugaban kasar Bangladesh. Tare da Shugaba Ziaur Rahman, ya ba da gudummawa ga kafa Kungiyar Kudancin Asiya don Haɗin Kai na Yankin (SAARC) a cikin 1980.
|