Muhammad Al-Tunji ( Larabci: محمد ألتونجي/Muḥammad Alūnjī; – 1933) masanin ilmin harsunan Siriya kuma marubuci. Ya sami digirin digirgir (PhD) a harshen Farisa a jami'ar Tehran a shekarar 1966 sannan ya sami digirin farko a fannin adabin larabci a jami'ar Damascus a shekarar 1955 kuma ya sami babban digiri na uku a fannin adabin larabci daga jami'ar Saint Joseph. [1] [2] Ya sami lambar yabo ta Indiya daga UNESCO a shekara ta 1970 kuma ya sami kyauta daga shugaban jami'ar Aleppo a shekara ta 1986 kuma ya sami kyauta daga shugaban jami'ar Benghazi a shekara ta 1989. [2]
Ya kasance Farfesa kuma Mataimakin Farfesa a wasu jami'o'i kamar: Jami'ar Damascus (1966-1970), Jami'ar Benghazi (1971-1975), Jami'ar Aleppo (1975-1976). Ya yi wata uku yana koyar da harshen Larabci a ƙasar Sin a shekarar 1979. Ya kasance malami mai ziyara a wasu jami'o'i kamar Jami'ar Budapest (1982), Jami'ar Exeter (1984). [1]
Bibliography
- Mu jam a lam matn al-hadith man warad dhikruhum fi hadisi [3]
- Sha irat fi asr al-Nubuwwah [3]
- Kamus na Larabci na Farisa (1993) [1] kuma ya fassara "The Golden Dictionary" na Muhammad Al-Tunji [4]
- Asma'ul Kutub [5]
- Diwan al-Amir Abi Firas al-Himdani
- Al-Mujam al-Mufassal fi Tafsir Gharib [6]
Manazarta
- ↑ 1.0 1.1 1.2 Muhammad Tunji Archived 2018-10-08 at the Wayback Machine, Web Site
Iranology Foundation.
- ↑ 2.0 2.1 جریدة شرق الأوسط. Arabic international newspaper headquartered in London, Asharq Al-Awsat
- ↑ 3.0 3.1 Muhammad al-Tunji, books of Muhammad al-Tunji in Amazon.
- ↑ behindthename, Meaning & History of SHAKEEB (to english languages) .
- ↑ Modern Arabic manuscripts in the National Library of Tunis, in MME 4 (1989), pp. 56-66. (pdf ) 1988:,
- ↑ The Arabicized Turkish Word in the Qur’an: A Study of “Ghassaq”,
Al-Tunji and Muhammad., 2003
Al-Tunji, Muhammad. (2003). Al-Mujam al-Mufassal fi Tafsir Gharib al-Qur’an al-Karim. Lubnan: Dar al-Kutub al-Ilmiyyah.