Joko Widodo ko Jåkå Widådå ko Jaka Widada, (an haife shi a 19 ga Yuni 1961), an kuma sanshi da Jokowi, dan siyasa ne a ƙasar Indonesiya kuma tsohon dan kasuwa.
Jokowi mamba ne a jam'iyyar siyasa ta Democratic Party of Struggle (PDI-P)'. Ya fara tashen sa ne daga zama magajin garin Surakarta daga Yuli 28, 2005 zuwa Octoba 1, 2012. sannan ya zama gwamnan Jakarta daga Octoba 15,2012 har ya zuwa Oktoba 16 2014.
Ya zama shugaban Indonesiya a watan Oktoba na 2014, mataimakin sa shine Jusuf Kallah. Jokowi ya sake tsayawa takara a zaben watan Afrilu na 2019. An haifi Joko Widodo a Surakarta tsakiyar tsuburin Java a kasar Indonesiya. Shi Musulmi ne. Ya auri matar sa Iriana tun 1986, suna da yaya uku. Yayi karatu a jami'ar Gadjah Mada inda ya karanta ilimin sanin dazuzzuka.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.