Amina Khalil ( Larabci: أمينة خليل; an haife ta a ranar 26 ga watan Oktoban shekarar 1988) 'yar wasan fina-finan Masar ce kuma 'yar wasan talabijin wacce ta yi fice a ƙarshen 2010s da farkon 2020 a cikin ƙasashen Larabawa. [1][2] Shawarar da ta yi game da yancin mata ya ba ta lambar girma ta jakadiyar Asusun Majalisar Ɗinkin Duniya (UPFA) a Masar.
Rayuwar farko
Khalil ta yi karatun acting a The American University da ke Alkahira kuma ta kammala a shekarar 2009. Ta yi karatu a Lee Strasberg Theater and Film Institute a New York City. [2] Ta yi karatun ballet tun tana ƙarama har zuwa shekara ta 17.
Sana'a
Matsayinta a cikin fina-finan Ashham (2012), Khetta Badeela (2015) da Sukkar Mor (2015) sun sami yabo sosai. [3] Matsayinta na (breakout role) a cikin nunin talabijin na shekarar 2016 Grand Hotel (wanda kuma aka sani da Sirrin Kogin Nilu), da jerin shirye-shiryen TV na 2018 Layalie Eugenie (Eugenie Nights), duka suna kan Netflix. [1] Ta yi rawar gani a Taraf Tallet, Sharbat Loze, Nekdeb Law Olna Mabenhebesh, Saheb El Saada da Wallei El Ahd. [3]
Ta ambaci Marion Cotillard a matsayin zuriyarta ta wasan kwaikwayo, [1] kuma ta ce tana son yin jagora a cikin wani fim ɗin wasan kwaikwayo wanda shine "Salon Lara Croft, ko kuma kamar Jennifer Lawrence a cikin Wasannin Yunwa". [1] Ta yi waka tare da mawakin hip hop na ƙasar Masar Zap Tharwat. [4]
Rayuwa ta sirri
A watan Yulin shekarar 2020, ta yi aure da hamshakin ɗan kasuwa kuma injiniya Omar Taha. [5] Ayyukanta sun haɗa da kitesurfing da swimming. [1]
A cikin watan Oktoba 2020, Khalil ta yi fama da COVID-19 kuma tun daga lokacin ta murmure. [6]
Ita ce mai ba da goyon baya ga mata da lafiyarsu a Masar, kuma a cikin watan Yuni 2021 Asusun kula da yawan jama'a na Majalisar Ɗinkin Duniya ya naɗa ta jakadiyar fatan alheri. [7]