Yauri
Yauri, karamar hukuma ce dake a Jihar Kebbi, Arewa maso yamman Nijeriya.[1] Yauri na daya daga cikin jerin garuruwa da rafin neja (River Niger) ya ratso a ciki, wannan ya saka sana'ar Su yake daya daga cikin sana'o'i da ake gudanarwa a garin. Musamman kabilan salkawa wadanda su aka fi sani da kamun kifi. Yauri ta tara kabila da yaruka kala-kala, daga cikin su akwai gunga ( ko kuma gungawa), kambari, salkawa, da sauransu. Yauri nada cikin shekaru 600 (daga 1460s-2020) sarakuna 42 wanda sarki Dr. Muhammad Zayyanu Abdullahi CON, FNSM shine bisa karagar mulki. [2] DemographicsKabilun da ke zaune a Yauri sun haɗa da Shangawa, Gungawa, Dukawa, Kamberi, Hausawa, Nupe, Yarbawa da kuma Kanuri. Sai dai, rinjayar da Hausawa suka samu a tsarin siyasa da zamantakewar Arewacin Najeriya ya sa wasu daga cikin manyan kabilun Yauri suka fara karɓar al'adun Hausawa, wanda hakan ya haifar da Hausancewar wasu daga cikinsu. A halin yanzu, Hausawa ne suka fi rinjaye a shugabancin Yauri. Manazarta
|