Umar Ibn Sa'ad
![]() 'Umar ibn Sa'ad ( Larabci: عمر بن سعد ) ( fl. 620-686), ya kasan ce ɗa ne ga Sahabin Muhammad Sa'ad ibn Abi Waqqas . An haifeshi a garin Madina sannan daga baya ya koma garin Kufa wacce mahaifinsa ya gina kuma ya kasance a wurin har zuwa rasuwarsa. Malami ne, kuma yana karbar umarni daga Ibn Ziyad . Yana daga cikin shugabannin sojojin da suka kashe Husayn bn Ali a yakin Karbala a shekara ta 680, babban yakin farko na yakin basasar Musulunci na biyu (Fitna ta biyu). Matarsa ‘yar uwar Mukhtar al-Thaqafi ce, wacce ta mulki kasar Iraki daga shekarar 685 zuwa shekarar 687, a lokacin Fitina ta Biyu . Ya kuma haifi da, Hafs Bin Amar bin Saad bin Abi Waqqas, wanda ya kasance a bisa tarihi da mahaifiyarsa ta kashe a lokacin gwamnatin Mukhtar al-Thaqafi. Abu Amra Kaysan ne ya kashe Umar bn Sa’ad, bisa umarnin Mukhtar al-Thaqafi, saboda ya shiga yakin Karbala.[1][2] Manazarta |