Toulou Kiki (an haife ta ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1983) jaruma kuma mawakiya yar kasar Nijar ce. An zabe ta a matsayin fitacciyar jarumar fim ta Afrika wato gasar Africa Movie Academy Award for Best Actress in a Supporting Role saboda fim din da tayi maisuna Timbuktu a shekarar 2014.
Tashe
A shekarar 2014 ta baiyana da suna "Satima" a fim din Timbuktu.[1] Fitar da ta bata damar zama shiga gasar fina-finai a Afrika gasar 11th Africa Movie Award inda tayi rashin nasara a hannun Hilda Dokubo.[2]
Manazarta