Share to: share facebook share twitter share wa share telegram print page

Sarkin Nuhu Muhammad Wabi

Sarkin Nuhu Muhammad Wabi
Rayuwa
Haihuwa Jama'are, 1961 (63/64 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar, Jos
Harsuna Hausa
Sana'a
Sana'a sarki

Tarihin sa

An haifi Sarkin Nuhu Muhammad Wabi ne a shekarar dubu daya da dari tara da sittin da daya (1961), wanda ya kasan shine Babban ɗa kuma yarin Jama'are tun kafin rasuwar mahaifin nasu Sarki Muhammad wabi. Sarki Nuhu Muhammad Wabi shine Sarkin Jama'are dake jihar Bauchi a Najeriya, Ya samu sarautar ne bayan Rasuwar mahaifin sa Sarki Muhammad wabi iv Dan Muhammad wabi[1]. Marigayin Sarkin Alhaji Muhammad wabi iv ya rasu ne a ranar 5 ga wadan Febreru na shekarar 2020, wanda ya kasance yayi mulki ne wanda ya shafe sama da shekaru 52 akan mulki.[2]

Fadar Sarkin Jama'are

Karatun sa

Ya yi makarantar firamare ta Jama’are Central; Makarantar Sakandaren Gwamnati Kuranga Azare da Jami'ar Jos. [3]

Ayyukan sa

Sabon sarkin ya yi aiki da ma’aikatar ayyuka ta tarayya na tsawon shekaru hudu kafin ya koma ma’aikatan gwamnatin jihar Bauchi a matsayin jami’in gudanarwa. Ya yi ritaya a 2013 a matsayin sakatare na dindindin. [4]

Manazarta ta

  1. https://kingdomsofnigeria.com/2018/08/18/emir-of-jamaare/
  2. https://dailytrust.com/bauchi-gov-okays-nuhu-wabi-as-new-emir-of-jamaare/
  3. https://dailytrust.com/bauchi-gov-okays-nuhu-wabi-as-new-emir-of-jamaare/
  4. https://dailytrust.com/bauchi-gov-okays-nuhu-wabi-as-new-emir-of-jamaare/
Kembali kehalaman sebelumnya