Muhammad Sani Abacha. An haife shi ne a ranar 20, ga watan Satumba, a shekara ta alif ɗari tara da arba'in da uku (1943A.C) Miladiyya.[1] Shi tsohon Janar ne na soja. Haifaffen Kano[2], da ke Arewacin Najeriya (a yau jihar Kano). Ya kuma mutu a ranan talata 8, ga watan Yuni a shekara ta alif ɗari tara da chasa'in da takwas 1998.[3] Sani Abacha shugaban Ƙasar Najeriya[4] ne daga watan Nuwamba, a shekarar alif ɗari tara da chasa'in da uku 1993, zuwa watan Yuni shekarar alif ɗari tara da chasa'in da takwas 1998, (bayan Ernest Shonekan - kafin Abdulsalami Abubakar).[5]
Sani Abacha ya kasance shugaban hafsan sojojin ƙasa na Najeriya, tun daga shekarar alif ɗari tara da tamanin da biyar 1985, zuwa shekarar ta alif ɗari tara da chasa'in dai-dai 1990. sannan kuma shugaban tsaron Najeriya daga shekarar alif ɗari tara da chasa'in dai-dai 1990, har zuwa shekara ta alif ɗari tara da chasa'in da uku 1993, sannan daga bisani kuma Ministan Tsaro na ƙasa.
Matakan da ya kai a Soja.
Shekara
Bajen mataki
Girma
1963
Second lieutenant (Commissioned)
1966
Lieutenant
1967
Captain
1969
Major
1972
Lieutenant colonel
1975
Colonel
1980
Brigadier general
1984
Major general
1987
Lieutenant general
October 1990
General
Mutuwa
A ranar 8, ga watan Yuni a shekarar alif ɗari tara da chasa'in da takwas 1998, Abacha ya rasu a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock Villa dake Abuja[6]. An yi jana’izarsa a wannan ranar kamar yadda addinin musulunci ya tanada ba tare da tantance gawar shi ba, wanda hakan ya kara rura wutar hasashen da ake yi na cewa kashe shi akayi.[7] Sai dai Gwamnati ta bayyana dalilin mutuwarsa a matsayin bugun zuciya wanda ya taso mashi ba zato ba tsammani.[8] Jami'an diflomasiyya na ƙasashen waje, ciki har da manazarta leƙen asirin Amurka[9], sun bayyana cewa mai yiwuwa an sanya masa guba ne. Babban jami’in tsaronsa Hamza al-Mustapha ya yi imanin cewa wasu jami’an Isra’ila ne suka sanya masa guba a cikin kamfanin Yasser Arafat ta hanyar gaisawa (wato Nussbaum) daga wannan lokacin ne kuma ya fara ganin canji a jikin shugaban.[10] Wanda har ake tunanin an sanya masa guba ne a Tuffa (Apple). Kafin mutuwarsa, yana gab da miƙa mulki ga gwamnatin farar hula a watan Oktoba shekarar alif ɗari tara da chasa'in da takwas 1998, wanda aka aiwatar a watan Oktoban shekarar alif ɗari tara da chasa'in da biyar 1995.[11] Bayan rasuwar janar Sani Abacha, Janar Abdulsalami Abubakar ya zama shugaban ƙasa, wanda A dalilin gajeren wa'adinsa yasa aka samu Jamhuriyar Najeriya ta huɗu.[12]