Rachid El Ouali (Larabci: رشيد الوالي an haife shi a ranar 3 ga watan Afrilu, 1965) shahararren ɗan wasan kwaikwayo ne, furodusa, darekta kuma mai watsa shirye-shiryen TV.
Sana'a
El Ouali ya fara wasan kwaikwayo ne a karshen shekarun 1980. Ya nuna gwaninta a cikin babbar rawar da ya taka a wasan kwaikwayo na TV serial Flock of Pigeons (سرب الحمام, Serb Al Hamam). Ya zama tauraro a cikin shahararren wasan kwaikwayo na talabijin Hossein & Safia (الحسين و الصافية، El Hossein w Safia) tare da 'yar wasan kwaikwayo Samia Akariou. A cikin shekarar 2006 Rachid El Ouali ya yi aiki a cikin wasan kwaikwayo na TV-serial Al Mostadaafon ( المستضعفون, The Underdogs) tare da 'yar wasan kwaikwayo Rajae Imran. Ya kuma zama tauraro a cikin fina-finai da dama da suka samu nasara kamar su Obsessions After Midnight (هواجس بعد منتصف الليل، Hawajes baada montassaf el leil), fim ɗin ban tsoro inda ya ɗauki babban matsayi tare da jaruma Majida Benkirane. Bayan aikin wasan kwaikwayo, ya kuma ba da umarni ga gajerun fina-finai da sitcomu da dama kamar: Ninni ya Moummou, Nass El Houma, L'Aube, da La mouche et moi.[1]