Rachel Sibande
Rachel Sibande, (an haife shi a ranar 9, ga watan Janairu 1986, a Lilongwe, Malawi) ƙwararriya ce masaniyar kwamfuta kuma 'yar kasuwan zamantakewa. Ita ce ta kafa mHub, cibiyar fasaha da incubator don masu ƙirƙira da ƴan kasuwa masu tasowa.[1][2] Ita ce mai ba da shawara kan fasaha, wacce ta karɓi tallafin karatu na Google Anita Borg.[3] A shekarar 2016, an naɗa ta ɗaya daga cikin ’yan kasuwa 30 da suka fi fice a Afirka a 'yan ƙasa da shekaru 30 da Forbes ta wallafa.[4] Sibande ta ba da gudummawar haɓakawa da tura sabbin hanyoyin fasahar fasaha a cikin aikin gona, kiwon lafiyar jama'a, sa ido kan zaɓe, haɗin gwiwar jama'a, gudanar da bala'i da Sabis na Kuɗi na dijital a cikin ƙasashe 18. Ya shafi ilimi, ci gaba da yankunan kasuwancin, zamantakewa.[5] Rayuwar farko da ilimiTana da shekaru 15, ta halarci Kwalejin Chancellor na Jami'ar Malawi. Ta kammala karatun digiri na farko, inda ta karanci kimiyyar kwamfuta.[6] Sibande ta sami Jagoran Kimiyya (Master of Science) a ka'idar bayanai, codeing, da cryptography daga Jami'ar Mzuzu a cikin shekarar 2007 tare da bambanci (distinction).[6] ![]() Ta sami digiri na uku a fannin kimiyyar kwamfuta daga Jami'ar Rhodes a shekarar 2020 a matsayin Google Scholar. Sana'aRachel Sibande tana aiki a matsayin Babbar Daraktar, Bayanai don Ci gaba. Ta ƙaddamar da yunƙuri don haɓaka ƙwarewar dijital tsakanin yara, 'yan mata, matasa, da mata. A baya ta yi aiki a matsayin Darakta na kungiyoyi masu zaman kansu na ACDI/VOCA, Agribusiness Systems International, da Palladium Group akan ayyukan ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a gabashin Afirka.[6] Girmamawa da kyaututtuka
Rayuwa ta sirriSibande ta auri Chrispine Sibande, lauya mai kare hakkin ɗan Adam ɗan Malawi.[7] Suna da 'ya'ya uku. Manazarta
|