Muhammad Sanneh
Muhammed Sanneh (an haife shi a ranar 19 ga watan Fabrairu a shekara ta 2000) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Gambia wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Baník Ostrava. Sana'aA ranar 2 ga watan Fabrairu a shekara ta 2019, Sanneh ya bar ƙasarsa ta Gambia kuma ya sanya hannu kan kwangilar ƙwararru tare da Paide. [1] A cikin watan Disamba a shekara ta 2020, an sanya shi cikin ƙungiyar Meistriliga na kakar saboda rawar da ya taka a kakar shekarar 2020.[2] Ya shiga tawagar Czech Baník Ostrava a cikin watan Janairu a shekara ta 2021. [3] Ya fara wasansa na farko na ƙwararru tare da Baník Ostrava a wasan 1 – 1 Czech First League da Bohemians 1905 a ranar 16 ga watan Afrilu a shekara ta 2021. [4] Baník Ostrava ya kunna batun siyan sa akan lamunin nasa, don ci gaba da kasancewa tare da kulob din bayan kakar 2020 zuwa 2021 a ranar 17 ga watan Afrilu a shekara ta 2021.[5] Loan a PohronieA cikin watan Janairu a shekara ta 2021, Sanneh ya sanya hannu kan lamunin rabin kakar tare da kulob ɗin Pohronie.[6] Ayyukan kasa da kasaA watan Yuni a shekara ta 2020, Sanneh ya sami kiransa na farko ga babban tawagar ƙasar Gambia.Ya buga wasa a Gambia a wasan sada zumunta da suka doke Togo da ci 1-0 a ranar 8 ga watan Yuni a shekara ta 2021.[7] Rayuwa ta sirriKanin Sanneh Bubacarr shima kwararren dan wasan kwallon kafa ne. [8] Manazarta
Hanyoyin haɗi na waje
|