Muhammad Bello Yabo
Muhammad Bello Aliyu Yabo wanda aka fi sani da Bello Yabo (an haife shi a ranar 1,ga watan Junairu shekara ta 1962). Malamin Addinin Musulunci ne a Najeriya kuma ana lissafo shi cikin manyan malaman Najeriya. Malam Bello Yabo ya kuma soki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan rashin tsaro a Arewacin Najeriya, wato (Arewa maso Yammacin Najeriya) musamman a jihohin Zamfara, Sokoto, Kaduna, Katsina da Jihar Neja.[1] Ilimi da AikiBello Yabo ya yi makarantar Islamiyya tun yana ƙarami. Bayan ya kammala sai Malam Bello Yabo ya fara makarantar firamare a makarantar firamare ta garin Yabo daga bisani ya wuce makarantar Government Day Secondary School duka dai a garin na Yabo. An kuma naɗa Bello Yabo a matsayin mai ba da shawara na musamman kan kula da hanyoyin karkara.[ana buƙatar hujja] Ya yi aiki a matsayin mai kula da kuɗi na cikin gida a ƙaramar hukumar Dange-Shuni, ya riƙe Daraktan kuɗi na musamman na asibitin Sokoto, daraktan kuɗi ma'aikatar ilimi ta Sokoto. Sheikh Bello yabo yana cikin sahun malamman da suka yi yaƙi da Akidar boko haram a Nigeria. Sukar El-Rufa'iA shekara ta 2020 yayin da annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta ɓulla a jihar Sokoto, Bello Yabo, babban malamin addinin Islama na jihar Sokoto, bayan wani faifan bidiyo ya bayyana a soshiyal midiya yana kiran sauran mabiya addinin Musulunci da su fito ƙwansu da ƙwar-ƙwarta su don Sallar Eid-el-Fitr bayan sun yi azumin watan Ramadan.[2] Wanda har ya nuna cewa cutar bata yaɗu ba a Najeriya saboda haka babu dalilin da za'a hana mutane yin Addinin su. Haka kuma a wani wani faifan bidiyo wanda kuma ya yi Allah wadai da hana Sallar Idi, a Jihar Kaduna. Wanda a faifan bidiyon ya caccaki Gwamnan jihar Kaduna El-Rufae da sauran gwamnoni kan hana Sallar Idi a jihohinsu. Rundunar ƴan sandan Najeriya ta gayyaci Bello Yabo saboda wannan faifan bidiyon na rana ɗaya wanda ya sifanta gwamnan Kaduna El-Rufa'i da "ɗan ƙaramin tsuntsu".[3][4][5][6][7] Duba kumaManazarta
|