Cif Michael Adeniyi Agbolade Ishola Adenuga Jr CSG GCON[1] (an haifeshi ranar 29 ga watan Afrilu, 1953) hamshakin attajirin ɗan kasuwa ne a Najeriya, kuma mutum na uku mafi arziki a Afirka.[2][3] Kamfaninsa na Glo (kamfani) shine babban kamfanin sadarwa na biyu mafi girma a Najeriya, wanda ke da aiki a kasashen Ghana da Benin. Ya kuma mallaki hannayen jari a bankin Equitorial Trust Bank da kuma kamfanin hakar mai na Conoil (tsohon kamfanin hada hadar mai). Forbes ya kiyasta darajarsa ta dala biliyan 6.2 zuwa Mayun shekarar 2021.
Rayuwar farko da ilimi
Mahaifinsa, da Oloye Michael Agbolade Adenuga Sr, malamin makaranta ne, yayin da mahaifiyarsa, Omoba Juliana Oyindamola Adenuga (nee Onashile, na Okesopin, Ijebu Igbo ), ya mai yar kasuwa na sarauta Ijebu lõkacin saukarsa.[4]
Adenuga yayi karatun sakandare a makarantar Ibadan Grammar School, Ibadan, jihar Oyo, Najeriya da Comprehensive High School, Aiyetoro, don samun babbar takardar shedar kammala karatun sakandare (HSC). Ya yi aiki a matsayin direban tasi don amfani da kuɗi wurin karatun jami'ar shi.[5] Ya kammala karatunsa daga Jami'ar Arewa ta Yammacin Oklahoma da Jami'ar Pace, New York, tare da samun digiri a fannin Gudanar da Kasuwanci.
Ayyuka
Adenuga ya samu miliyan karon farko a shekarar 1979, yana da shekaru 26 a lokacin, yana siyar da yadin (lace) da kuma rarraba kayan lemu (soft drinks).[6] A shekarar 1990, ya sami lasisin hako (fetur) kuma a shekarar 1991, Kamfaninsa na Consolidated Oil ya haƙo mai a cikin zurfin ruwan da ke yankin Kudu maso Yammacin Jihar Ondo, kamfani na farko ɗan asalin kasar da ya yi hakan a kasuwanci.
An ba shi lasisin GSM a sharaɗance a cikin 1999; bayan an soke bashi iznin a baya. Yazo na biyu lokacin da gwamnati ta sake yin wani gwanjo a shekarar 2003.[7][8] Kamfanin sadarwa na Globacom ya bazu cikin sauri kuma ya fara ƙalubalantar katafaren kamfanin MTN. Ta ƙaddamar da aiyuka a Benin a cikin 2008, kuma ta ci gaba da bazu a ƙasashen Ghana da Cote d'Ivoire, tare da ƙarin lasisi a halin yanzu ana sa ran wasu ƙasashen Afirka ta Yamma.
An anbatashi shi a matsayin gwarzon ɗan kasuwar Afirka na Shekara a bikin farko na Kyautar Telecoms na Afirka (ATA) a watan Agusta shekarar 2007[9]
A watan Mayu na shekarar 2015, Adenuga ya sayi kwangilar sayan kamfanin sadarwa na Ivory Coast Comium Cote d'Ivoire kan dala miliyan 600.[10]
Daraja
A shekarar 2012, gwamnatin Najeriya ta karramashi da Grand Commander of the Order of the Niger
.[11]
Ya riƙe muƙamin tribal chief na Otunba Apesin ga mutanen ƙabilar Mutanen Ijebu.[12]
A cikin shekarar 2018, Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi masa ado da tambarin Kwamandan Sojoji.[13]
Adenuga ya kasance dayya daga cikin Manyan mutane 100 da suka fi tasiri a Afirka, a bayyana haka a mujallar New African a shekarar 2019.[14]
Duba kuma
Manazarta
Hanyoyin haɗin waje