Jennifer Driwaru
Jennifer Driwaru (an haife ta a shekara ta 1982) 'yar siyasa ce kuma 'yar kasuwa 'yar ƙasar Uganda, wakiliyar mata a gundumar Maracha a majalisar dokokin Uganda ta 11 da ke da alaƙa da jam'iyyar National Resistance Movement (NRM). [1] [2] Tarihi da ilimiAn haifi Driwaru kuma ta girma a ƙaramar hukumar Yivu, Loinya Parish a ƙauyen Aliro Gabas ɗiya ce ga Orijaba John, wani kwamandan ‘yan sanda mai ritaya wanda ya yi aiki a matsayin kwamandan ‘yan sanda (DPC) da kuma Florence Drijaru, ‘yar kasuwa. [3] A shekarar 1995, Driwaru ta kammala Jarabawar Firamare (PLE) a Makarantar Firamare ta Maracha, a matakin O a shekarar 1999 da A level (ta yi LEG/Fine art) a shekarar 2001 daga Makarantar Sakandare ta Maracha. A cikin shekarar 2004, ta yi difloma a fannin ilimi tare da zane-zane sannan ta shiga Jami'ar Kyambogo inda ta sami digiri na farko a Guidance And Counseling a shekarar 2012, difloma na gaba a Social Work and Social Administration a shekarun 2014 zuwa 2015. [2] AikiTa yi aiki a matsayin malama, tana koyar da harshen Ingilishi a makarantar sakandare ta Maracha sannan ta yi aiki a asibitin St. Joseph's Hospital Maracha/Ovujo Hospital a matsayin ma'aikacinyar zamantakewa tsakanin shekarun 2022 zuwa 2013.[4] A cikin shekarar 2007, Jennifer kuma ta yi aiki tare da Baylor Uganda a Entebbe a matsayin mai ba da shawara tare da ƙwararrun PHAs.[5] Ta kuma yi aiki da Hukumar Rajistar Shaida ta Ƙasa (NIRA) a matsayin jami’ar yin rajista a shekarar 2014 sannan a matsayin ma’aikaciyar jin daɗin jama’a tare da Kwamitin Ceto na Duniya (IRC) tsakanin shekarun 2017 da 2019. [1] Sanannun ayyukaDriwaru ta sayi motocin ɗaukar marasa lafiya guda biyu a gundumar Maracha daga cikin kuɗin da aka ce aka ba ta don sayen mota.[3] [6] Duba kumaJerin sunayen 'yan majalisar dokoki na goma sha daya na Uganda Manazarta
|