Hausa Bakwai: Wata zuri'a ce me ɗinbin tarihi a ƙasar Hausa wadda kuma ta fito daga tsatson ɗan Bayajidda mijin sarauniya Daurama me suna (Bawo).[1]
Waɗannan sune ƙasashen Hausa bakwai kamar haka: 1. Daura 2. Kano 3. Katsina 4. Zazzau (Zaria) 5. Gobir 6. Rano 7. HadejiaBiram(Garun Gabas)[2] Akwai kuma waɗanda ake kira da Banza Bakwai. Banza bakwai daga baya Masarautar Daura ta bakin Wakilin Tarihi na masarautar an sauya sunan zuwa ƴan'uwa bakwai ko kuma a ce musu Ƙanne bakwai. Su kuma sun fito ne daga tsatson Karaf-da-gari dan da Bayajidda ya haifa da baiwarsa Bagwariya.