Kwalejin Ilimi ta Jihar Zamfara makaranta ce ta gaba da sakandare ta gwamnatin jihar da ke garin Maru a jihar Zamfara,Najeriya .Shugaban makarantar na yanzu shine Ibrahim Usman Gusau.
Tarihi
An kafa Kwalejin Ilimi ta Jihar Zamfara a shekarar 2000. A da ana kiranta da ‘Teachers’ Training College (TTC)’, daga baya kuma aka canza ta zuwa ‘Advanced Teachers’ College (ATC)’ daga baya kuma aka canza mata suna zuwa Kwalejin Ilimi ta Jihar Zamfara.