Hashil Twaibu Abdallah malami ne a fannin ilimi na ƙasar Tanzaniya kuma a halin yanzu shi ne babban sakataren kasuwanci da masana'antu a Tanzaniya. Ya kasance mataimakin babban sakataren kasuwanci da masana'antu da shugaba Samia Suluhu Hassan ta naɗa a ranar 6 ga watan Afrilu, 2021.[1][2][3][4][5] Ya kasance Mataimakin Dean a Sashen Shari'a kuma Shugaban Sashen Shari'a a Open university Tanzaniya sama da shekaru goma.[6][7][8]
Sana'a
A shekara ta 2003, ya sami Diploma a fannin shari'a daga Cibiyar Nazarin Shari'a, Bachelor of Law a shekara ta 2007 daga Jami'ar Zanzibar da Difloma a fannin Shari'a a shekarar 2008 daga Makarantar Shari'a ta Tanzaniya. Ya samu digirinsa na biyu a fannin ilimi a shekarar 2010 da kuma Doctor of Philosophy in Law (PhD) daga Jami'ar Katolika ta Ruaha. Shi ne kuma mai ba da shawara na Babbar Kotun Tanzaniya, memba na Tanganyika Law Society da East Africa Law Society.[9][10]
Ayyukan da aka zaɓa
Abdallah, Hashil; Wawa, Anna (December 2019). The Role of ODL System in Promotion and Protection of the Right to Education for Women in Tanzania:Challenges and Prospects. SemanticScholar. S2CID 233340650.[11][12]
Duba kuma
Elifas Bisanda – Vice Chancellor of Open University of Tanzania
Tolly Mbwette – Tanzanian academic (1956-2020)
Irene Tarimo – Tanzanian scientist, biologist and educator