Chris Iheuwa ɗan wasan kwaikwayo ne na Najeriya, mai shirya fina-finai kuma ɗaya daga cikin jagororin masana'antar Nollywood.[1][2] Shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar Actors Guild of Nigeria.[3] An san shi dalilin Irin rawar da ya taka a cikin Rattle Snake (1995), Phone Swap (2012), Joba (2019), The Second Bed (2020), La Femme Anjola (2020), Stranger (2022).[2][3][4]
Ilimi
Ya yi digirinsa na farko a fannin wasan kwaikwayo a Jami'ar Ibadan da digiri na biyu a Jami'ar Legas.[2][3]
Rigimar sace mutane
An kusa sace Iheuwa a shekarar 2021. An yaudare shi zuwa wani wuri da ba a san ko ina ba a birnin Fatakwal inda daga karshe ƴan sanda suka ceto shi.[5]
Fina-finai
Manazarta