La Femme Anjola fim ne da aka fitar a shekara ta 2021 wanda Tunde Babalola ya rubuta kuma Mildred Okwo ya ba da umarni. Fim ne mai ban sha'awa wanda jarumai Rita Dominic da Nonso Bassey suka taka rawa. [1][2] An sake shi a silima a ranar 19 ga Maris, 2021.
Takaitaccen bayani
La Femme Anjola ya ƙunshi labari akan wani dillalin hannun jari wanda ya faɗa soyayya da wata hatsabibiyar mace. Anjola tana auren wani ɗan-daba wadda ya mallaki gidan rawan inda take yin wasan da daddare.
Kungiyar mutum uku na Mildred Okwo, Tunde Babalola da Rita Dominic sun sake haɗuwa don shirywa wannan wasa tun lokacin da suka fitar da fim tsohon fim din su a shekara ta 2012, wato The Meeting.
An bayyana cewa an cire fim ɗin daga gidajen sinima na Film House da ke duk fadin Najeriya don haska fim ɗin Prophetess.[3] Da yake magana a wata hira da jaridar The Cable, darakta Okwo, ya dora laifi akan rashin tsari na masana’antar fina-finan Najeriya.[4] Ta sake bayyana cewa wannan dai sinima ne ya cire fim dinta na Surulere a shekara ta 2015, a cikin wani yanayi na rashin jituwa. Bayan jama'a sun nuna rashin jin dadin hakan ne Okwo, kuma ta bayyana cewa tana shirin fitar dashi ta kafar sadarwa na yanar gizo na kamfaninta ta yadda za'a kalla akan yanar gizo.[ana buƙatar hujja]