Babachir David Lawal (An haifeshi ranar 2 ga watan Agustan shekarar alif ɗari tara da hamsin da hudu 1954)[1][2] a kauyen Kwambla da ke karamar hukumar Hong a jihar Adamawa. Ya kasance sakataren gwamnatin tarayya daga ranar 27 ga watan Agusta 215 zuwa 19 ga watan Afrilu, 2017[3]
Farkon rayuwa da Karatu
Yayi karatun firamare a St. Patrick's , Maiduguri a shekarar 1969 ya wuce Nigeria Military School Zaria, daga 1970 – 1974 domin yin karatunsa na sakandare . Daga nan ya halarci Makarantar Koyon Ilimi ta ABU Zariya, daga shekarar 1974 zuwa 1975. Lawal , ya karanci Injiniyan Lantarki a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, kuma ya kammala a shekarar 1979 da Digiri na biyu (Electrical engineer)
Daga baya ya samu digirin digirgir a shekarar 2007.[4]
Aiki
Babachir ya fara aiki a kamfanin Delta Steel Company, Ovwian -Aladja inda ya kai matsayin Babban Injiniya , wannan ya kasance daga shekarar 1979 – 1984 . Daga nan ya yi aiki a Nigerian External Telecommunications Ltd, Lagos'a matsayin Babban Injiniya daga 1984 zuwa 1986. Ya kasance a Data Sciences Nigeria Ltd , daga 1986 zuwa 1989 , inda ya samu mukamin Manaja na Yanki , kafin ya tashi ya kafa kamfaninsa na Rholavision Engineering Ltd, Kaduna a shekarar 1990 .
Kafin ya kafa kamfanin sa na ICT da sadarwa a shekarar 1990.[5]
Ƙungiyoyi
- Memba a Nigeria Computer Society , NCS. Memba , Nigerian Society of Engineers, NSE, Memba a Majalisar Dokokin Injiniya a Najeriya , COREN. Memba , Cibiyar Gudanar da Ayyuka , PMI Memba, Cibiyar Nazarin Kasuwanci ta Duniya, IIBA Memba a Cibiyar Gudanarwa Canji, CMI
- Mataimakin Kodineta na Jiha , The Buhari Campaign Organisation, Jihar Adamawa 2002- 2005.
- State Coordinator ,The Buhari Campaign Organisation, Adamawa State , (2005 – 2010 )
- Memba , Congress For Progressive Change Committee National Contact and Mobilization Committee (2010 - 2013)
- Memba, Kwamitin Sabunta Canjin Cigaba na Majalisa, 2012
- Memba, All Progressive Change Change Commite , 2013
- Tsohon Babban Memba, Kwamitin Gudanarwa na Riko 2013 - 2014
- Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa na arewa maso gabas 2014.
- Memba, Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, 2015.[6]
Fagen siyasa
Babachir ya shiga siyasa a shekarar 2002 ta hanyar zama mamba a jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP).
ya rike ofisoshi da dama a jam'iyyar ANPP tun farko da kuma cikin tawagar yakin neman zaben Buhari ciki har da mataimakin Mai gudanarwa na kungiyar yakin neman zaben Buhari a jihar Adamawa.[7]
Sakatare
Shugaban Muhammadu Buhari ne ya naɗa shi a matsayin sakataren gwamnatin tarayya a shekarar 2015.[8] A ranar 30 ga Oktoban shekarar 2017, aka kore shi a matsayin sakataren gwamnatin tarayya bayan wani rahoto kan zargin sa da hannu wajen karkatar da kudaden agajin gaggawa.[9] Tare da maye gurbinsa da Boss Mustapha.
Manazarta