Amina Djibo Bazindre (an haife ta a ranar 28 ga watan Janairun shekara ta 1955) jami’ar diflomasiyyar Najariya ce. A ranar 5 ga watan Fabrairun shekara ta 2010, ta zama Jakadan Nijar a Rasha. [1]
Tarihin rayuwa
A cikin shekara ta 2005, Amina Bazindre an lasafta ta a matsayin Ambasadan Nijar a Hungary a shafin yanar gizon Ma'aikatar Harkokin Wajen Hungary . [2]
A ranar 5 ga Fabrairun shekara ta 2010, ta Kuma zama Ambasadan Nijar a Rasha . [1]
A watan Janairun shekara ta 2011, Angela Merkel da Christian Wulff suka karbe ta a matsayin Jakadiyar Nijar a Jamus . [3][4] Hakkokin ta sun hada da wakilcin diflomasiyya a Slovakia .
A watan Disambar shekara ta 2011, an kuma ba ta mukamin sufeto na ofishin diflomasiyya da kuma ofishin jakadancin Nijar. [5] A watan Afrilu shekarar 2013, an naɗa ta Babban Sakatare na hukumar kasa ta Francophonie . [6]
A shafin yanar gizon Ma'aikatar Harkokin Wajen Romania, Amina Bazindre an lasafta ta a matsayin Ambasadan Nijar a Romania (2018). [7]