Virgil Vries (an haife shi a ranar 29 ga watan Maris 1989) golane/mai tsaron ragan ƙwallon ƙafa ne na NamibiyaNamibia wanda ke taka leda a kulob din Moroka Swallows na Afirka ta Kudu.
Aikin kulob/Ƙungiya
A cikin watan Janairun 2012 an ba da rancensa zuwa ƙungiyar Carara Kicks ta Division 2. [1]
Daga baya a cikin shekarar 2012, ya sanya hannu kan kwangilar na ɗan gajeren lokaci tare da Orlando Pirates a gasar Premier ta Namibia. [2] A cikin watan Janairu 2013 ya tafi Maritzburg United FC a Premier Soccer League. Tun daga wannan lokacin ya buga wasanni 27 a kungiyar kuma ya ci gaba da kasancewa mai kokari a wasanni takwas kuma an cisa kwallaye 23 a wadannan wasannin.
Barin Kaizer Chiefs a cikin bazara 2019, [3]Virgil Vries ya shiga Moroka Swallows a ranar 26 ga watan Satumba 2019. [4]
Ayyukan kasa
Virgil Vries ya cancanci buga wa Namibia wasa. Ya buga wasansa na farko a kungiyar kwallon kafa ta Namibia a ranar 4 ga Yuni 2011 da kungiyar kwallon kafa ta Burkina Faso a ci 1-4 a Namibia. Tun daga 1 ga Yuni 2014 ya buga wa Namibia wasanni 11 kuma ya ci gaba da zama mai kokari a wasanni biyar.
Manazarta
Hanyoyin haɗi na waje