Usman Danjuma Shiddi (an haife shi a shekara ta alif 1967.[1] Wanda aka fi sani da Danji SS)[2] dan siyasan Najeriya ne kuma dan majalisa a halin yanzu mai wakiltar mazabar Ibi/wukari ta Jihar Taraba a majalisar wakilai ta tarayya a majalisar dokokin Najeriya.[3][4] A shekarar 2019 ya lashe kujerar dan majalisar wakilai da kuri'u 39,312 inda ya doke abokin hamayyarsa Yakubu Aliyara na jam'iyyar Action Alliance (AA) wanda ya samu kuri'u 22,147.[5][6] Shiddi shi ne Shugaban Kwamitin Tsaron Cikin Gida na Majalisar Wakilai ta Najeriya ta 9. kuma a shekarar 2020 ya sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress.[7]