An haifi Tahani Rached a ranar 16 ga watan Mayu, 1947, a Alkahira, Masar. A shekara ta 1966, ta koma Montreal don yin zane-zane. Ta kasance ɗaliba a École des beaux-arts de Montréal inda ta yi karatun zanen shekaru biyu.[1] Ta kara shiga cikin al'umma don haka ta koma harkar fim.[2]
Hukumar shirya fina-finai ta Kanada ta ɗauke ta aiki a matsayin ma’aikaciyar fim a shekarar 1981. Sai dai Rached ta bar hukumar fina-finai a shekarar 2004 inda ta koma Masar don yin fim.[3]
A cikin shekarar 2023 an naɗa ta a matsayin wacce ta karɓi Prix Albert-Tessier saboda nasarorin aikinta. [4]