Rikicin Jos na shekara ta 2008 ya kasance tarzoma ce da ta shafi kiristoci da musulmi dangane da sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranakun 28 da 29 ga watan Nuwamba 2008 a garin Jos dake yankin Middle Belt a Najeriya.[1][2] Rikicin na kwanaki biyu ya yi sanadin jikkata ɗaruruwa, yayin da aƙalla mutane 761 suka mutu.[3] An tura sojojin Najeriya (a yankin).[4]
Dalilai
Ma’aikatan zaɓe dai ba su fito fili sun bayyana sunayen waɗanda suka yi nasara a zaɓen ba, sai aka fara yada jita-jitar cewa ɗan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Barista Timothy Gyang Buba ne ya lashe zaɓen,[5] ya doke ɗan takarar jam’iyyar All Nigerian Peoples Party. Jama’ar al’ummar Hausawa Musulmi, sun fara gudanar da zanga-zanga tun kafin a fitar da sakamakon, wanda ya haifar da arangama da ta yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane tsakanin Musulmi da Kirista, wadanda suka fi goyon bayan Buba.[6]
Wai-wa-ye
Irin wannan tarzoma da aka yi a shekarar 2001 tsakanin Kirista da Musulmi a Jos ma ta yi sanadiyyar mutuwar ɗaruruwan mutane.[7] Rikicin 2004 a Yelwa, wani gari a Jihar Filato ya haifar da abin da ake kira Kisan Yelwa. Fadan da aka yi a jihar Kaduna ta arewa ta tsakiya a lokacin da aka yi yunƙurin kafa shari’ar Musulunci a shekarar 2000, ya haifar da raba garin Kaduna. Hakan ya biyo bayan tarzomar Kaduna a watan Nuwamban shekarar 2002, sakamakon yadda Najeriya ta karbi bakuncin gasar Miss World, wadda daya daga cikin wadanda suka fafata ta lashe gasar a bara.[8]
Tarzomar
Rikicin na kwanaki biyu ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 761,[3] sai kuma gidaje, masallatai, coci-coci da makarantu sun lalace ko an kona su.[9][10] Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya ta bayar da rahoton cewa mutane 10,000 ne suka tsere daga gidajensu saboda tarzomar,[2][11] kuma suna zaune a matsugunan da gwamnati ta samar na wucin gadi.[6] An tura sojojin Najeriya cikin birnin domin magance rikicin, gami da shiga a tsakanin Kiristoci da Musulmai.[12] An soke tashin jirage izuwa Jos, an kuma toshe hanyoyin arewa.[13]
Tasiri
Jonah Jang, gwamnan jihar Filato, ya sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a gundumomi hudu na birnin, kuma an ba sojoji damar "harbi" don hana sake afkuwar tashin wata tarzomar.[6] hukumar Human Rights Watch ta yi zargin cewa sojoji da ƴan sanda sun yi kisan gilla fiye da 130 a lokacin da suke mayar da martani kan tarzomar.[9] An kama matasa da yawa ɗauke da makamai na dukkan bangarorin biyu-(musulmai da kiristoci) a shingayen titin sojoji.[12] Ƴan sanda sun ce an kama sama da mutane 500 sakamakon tarzomar. Sai dai jami'an jihar sun ce babu wanda aka samu nasarar gurfanar da shi a gaban kuliya.[3]
Blench, RM, Daniel, P. & Hassan, Umaru (2003): Haqqoqin samun dama da tashe-tashen hankula a kan albarkatun gama gari a jihohi uku na Nijeriya. Rahoto ga Sashin magance rikice-rikice, Bankin Duniya (wanda aka fitar a Jos Plateau )