Mutanen Punic, yawanci ana kiransu Carthaginians[1] (kuma wani lokacin a matsayin Yammacin Phoenicia), mutanen Semitic ne waɗanda suka yi kaura wato hijira daga Phoenicia zuwa Yammacin Bahar Rum a lokacin Farkon da ake Kira da Iron Age . A cikin ilimin zamani, kalmar Punic, tayi daidai da kalmar Helenanci na kalmar Phoenician, ana amfani da ita ne kawai don komawa ga yaren Phoenicians a yammacin Bahar Rum, bin layin Gabashin Girka da Latin Yamma. Mafi girman mazaunin Punic shine Tsohon Carthage, amma akwai wasu mazauna 300 a bakin tekun Arewacin Afirka daga Leptis Magna a kasar Libya ta zamani zuwa Mogador a kudancin Morocco, da yammacin Sicily, kudancin Sardinia, kudancin da gabashin gabar Yankin Iberian Peninsula, Malta, da Ibiza. Harshensu, Punic, yare ne na Phoenician, ɗaya daga cikin yarukan Arewa maso Yammacin Semitic wanda ya samo asali ne Yankin Levant.
Tushen wallafe-wallafen sun ba da rahoton hujja Akan cewa lokuta biyu na mazauna Yankin Taya a yamma, na farko a cikin karni na 12 BC (biranen Utica, Lixus, da Gadir) wanda sunkasance masu Ilimin kimiyya fasaha na archaeology (ilmin bin diddiqi na binciken tarihin albarka tun kasa) Amma bai tabbatar da shi ba, kuma na biyu a ƙarshen karni na 9 BC, wanda aka rubuta a rubuce-rubuce akai a cikin Yankin gabas da yamma, wanda ya ƙare a cikin tushe da yankuna a arewa maso yammacin nahiyar Afirka (biranen Auza, Carthage, da Kition) [2] kuma sun zama wani ɓangare na hanyoyin na bunkasa kasuwanci da ke da ke da alaƙa da Taya, Arvad, Berytus, Sidon. citation needed] Kodayake an riƙe alaƙa Mai qarfi da yankin Phoenicia a duk tarihin su, sun kuma haɓaka alaƙar kasuwanci ta kusa da sauran mutanen yammacin Yankin Bahar Rum, kamar Sicilians, Sardinians, Berbers, Helenawa, da Iberians, kuma sun chigaba da haɓaka wasu halaye na al'adu daban da na ƙasarsu ta Phoenicia. Wasu daga cikin wadannan sun kasance sun raba ta duk mutanen yammacin Phoenicians, yayin da wasu aka ƙuntata su ga yankunan daban-daban a cikin yankin Yankin Punic.
Manazarta
- ↑ https://en.wikipedia.org/wiki/Punic_people#cite_note-1
- ↑