Musa bn Jafar,wanda aka fi sani da Al-Qazim (wanda ke sarrafa fushinsa) shi ne Imami na Shi'a na bakwai, bayan mahaifinsa Jafar bn Muhammad. Hakanan ana girmama shi sosai a tsakanin Ahlus-Sunnah, waɗanda suke masa kallon mashahurin malami. [1][2] An sami rarrabuwa a cikin Shiaswa kan batun Imamanci . Ismaili sun ce Ismail ibn Jafar, babban ɗan Jafar ibn Muhammad ya kamata ya zama imami na gaba yayin da babbar ƙungiyar Jafari (ko 'Yan- sha-biyu ) suka ɗauki Musa bin Jafar a matsayin limami na gaba.
Manazarta
↑Sharif al-Qarashi2, Baqir (2000). The Life Of Imam Musa Bin Ja'far aL-Kazim (PDF). Translated by Jasim al-Rasheed. Iraq: Ansarian.
↑A Brief History of The Fourteen Infallibles. Qum: Ansariyan Publications. 2004. pp. 135–143.