Mohammed Karim (1896 – 1972) ( Larabci: محمد كريم ) darektan fina-finan Masar, marubuci, kuma furodusa ne. Karim ya kawo Faten Hamama ta shahara a fim ɗin Yawm Said. Fim ɗinsa na shekarar 1946 Dunia an shigar da shi cikin bikin Fim na Cannes na 1946.[1]