Michael Kojo Essien (An haife shi a ranar 3 ga watan Disamban a shekara ta 1982) tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafan ƙasar Ghana ne wanda ya taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya kuma a yanzu haka memba ne na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Danish Superliga ta FC Nordsjælland. Har ila yau, ya buga wa tawagar kwallon kafa ta ƙasar Ghana wasa sama da sau (50).A lokacin da yake sharafin sa, a na ɗaukar Essien a matsayin ɗaya daga manyan 'yan wasan tsakiya na duniya.
Fara Ƙwallon Ƙafa
Essien ya fara wasansa ne da buga wa kungiyar Liberty Professional wasa a Ghana. A shekarar 2000, ya koma Faransa ya shiga Bastia, inda ya cinye kakar wasanni uku a nan kuma adadin wasannin da ya buga a nan sun kai 60, kafin ya koma ƙungiyar dake rike da kambun Ligue 1, wato Lyon a shekara ta 2003. A Lyon, Essien ya ci kofuna bi-da-bi a jere a shekara ta 2003 zuwa 2004 da 2004 zuwa 2005, kuma ya lashe kambun Lig 1, na Gwarzon Ɗan Wasan a Shekara ta 2005. A tsawon shekaru biyar da ya yi a Faransa, ya sami zama ɗan ƙasar Faransa. A cikin a shekara ta 2005, Essien ya sanya hannu tare da kungiyar Premier ta Chelsea A Chelsea, Essien ya taimaka wa kungiyar ta lashe gasar Premier a shekarar 2006 da 2010, da kuma kofunan FA uku da na League daya. Ya lashe gasar zakarun Turai a shekara ta 2012, yayin da yake sanya shi a matsayin wanda ya zo na biyu a gasar zakarun Turai na UEFA na shekarar 2008 . Ya lashe kyautar gwarzon Golan Chelsea a kakar sau biyu, a kakar shekarun 2006 zuwa 2007. da 2008 zuwa 2009.
Tarihin Rayuwa
An haifi Essien ne a babban birni Ghana Accra, iyayen sa su ne Aba Gyandoh da James Essien, Essien ya halarci Gomoa Nyanyano DC Primary and JSS. Ya fara wasan kwallon kafa ne bayan kammala karatunsa a Kwalejin St. Augustine da ke Cape Coast, yana wasa a wani kulob na gida da ake kira Liberty Professionals .
Ƙungiyoyin da Yayi Wasa
Bastia
Lyon
Chelsea
Real Madrid (aro)
Milan
Essien ya kulla yarjejeniya da kulob din Milan na Italiya kan kwantiragin shekara daya da rabi a ranar( 27) ga watan Janairun a shekara ta (2014) .
Panathinaikos
Persib Bandung
Sabil
A ranar 16 ga watan Maris a shekara ta (2019), Essien ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara daya da rabi tare da Sabail FK na Premier League na Azerbaijan, wanda kuma zai ga ya horar da kungiyar U(19) din su.
Wasa a Mataki na Duniya
Essien ya fara buga wasan farko a Gasar cin Kofin Kasashen Afirka da Morocco a ranar( 21) ga watan Janairun shekarar ( 2002). amma ya buga wa Ghana wasa a wasan sada zumunci da Masar a ranar( 4) ga watan Janairun shekarar( 2002) .
Aikin Horar da 'Yan Wasa
FC Nordsjælland
Salon wasa
Essien ya kasance ɗan wasan tsakiya mai ƙarfi, wanda sau da yawa yakan taka rawa a tsakiyar tsakiya . Sauda yawa ana yi masa magana a matsayin dan wasan tsakiya-zuwa-dambe saboda ikonsa na yin kuzari wajen tallafawa duka wasan zagi da na kare, da kuma karfin fada-a-ji da yake fuskanta, wanda ya sanya masa lakanin "The Bison". [1] Essien zai iya taka leda a matsayin mai tsaron gida, a dama na kariya da kuma a tsakiya . Baya ga yawan aiki, karfin jiki, da kwarewar kariya, Essien ya kuma mallaki fasaha mai kyau, hangen nesa, hazakar dabara, da halaye na jagoranci, kuma ya kasance mai karfin zura kwallaye daga nesa.
Rayuwar Kai
A watan Maris na shekarar( 2021), Essien ya nuna goyon bayansa ga 'yan LGBT a Ghana akan Twitter da Instagram . Daga baya ya goge rubutun bayan ya fuskanci suka daga wasu masu amfani da shafin na Ghana a dukkan bangarorin biyu.