Michael Bakari Jordan[1] (An haifeshi 9 ga Fabarairu a shekarar 1987) dan wasan kwaikawaiyon Amurka ne, mai shiryawa ne kuma mai bada umarni.
Tarihi
An haifi Micheal Bakari Jordan a ranan 9 ga watan Fabarairu a shekarar 1987 a Santa Ana dake jahar Kalifoniya[2], iyayenshi Donna da Micheal A. Jordan. Iyalin Jordan sunyi shekara 2 a Kalifoniya kafin su koma Newark dake jahar New Jersey.[2][3]. Yayi karatu a makarantar gaba da sakandire ta zane-zane ta Newark inda mahaifiyar shi tayi aiki kuma shi yayi kwallon hannu.[4][5] Jordan ya zauna a Las Anjalas a tun shekarar 2006.[6]