Makarantar Kwalejin Ilimi ta Tarayya Kontagora (FCE Kontagora) tana a jihar Neja , jahar dake arewa ta tsakiya Najeriya. An ƙirƙira/kafa makarantar a watan Satumba shekara ta 1978 a matsayin kwalejin malamai (Federal Advanced Teachers College, FATC) a lokacin Mulkin Olusegun Obasanjo (GCFR) mulkin soja kenan. Wannan ya faru ne bayan da Sir. Eric Ashby ya bada umurnin a ƙarƙashin dokar Najeriya mai no. 4 na shekara ta 1986, sai kuma aka dawo aka gyara shi a lamba no. 6 a shekarar 1993
An ɗaukaka matsayin kwalejin a ƙarƙashin Jami'ar Ilorin da kuma Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya.[1][2]
Tarihin shugabancin kwalejin
Mr. O. O. Ogun shine shugaban makarantar na farko a wani wajen da aka kafa makarantar a matsayin wucin gadi bana din-din-din ba a shekara ta 1978 a wannan lokacin duk wasu aikace-aikacen da koyarwa anayinsu ne a wajajen da hukumar makarantar ta kama haya ko kuma tayi aro a cikin garin Kontagora har yau-wajiya Malamai da Ɗaliban makarantar suna zama ne kodai haya ko kuma wani gurin da ba cikin makarantar ba a cikin gari. A shekara ta 1981 Dr. S K Afolabi an naɗa shi a matsayin muƙaddashin shugaban makarantar ya zauna a wannan matsayin har watan Disamba shekara ta 1982.
Sai kuma a watan Janairu shekara ta 1983. Dr. M A Uppal an tsammani ya zama shugaban makarantar bayan ya ɗau lokaci yana shugabantar makarantar na wuccin gadi, daga baya kuma sai aka maye gurbin shi da Dr. S A Abdurrahman a shekarar 1985 zuwa shekarar 1987. Bayan nan Alhaji Shehu Ɗalhatu ya zamo shugaban makarantar wanda yake da cikakken iko na shugabancin kwaleji har tsawon shekaru 6, wato tunda ya fara a shekarar 1987-1993 ya sauka.
A ranar 8 ga watan Maris shekarar 1993 Dr. Elisha G Kutara ya maye gurbin Alhaji Shehu Ɗalhatu a matsayin shugaban kwalejin, wanda ya rasa aikin shi daga Kwalejin Ilimi ta Zariya. Bayan nan an naɗa Dr. A. M Tura a matsayin shugaban kwalejin a shekarar 1996 a dalilin wani rikicin da ya dabaibaye makarantar wanda yayi dalilin har sai shugabannin Ilimi na ƙasa suka baki a rikicin kuma suka sake daidaita tsarin shugabancin kwalejin.
A ranar 1 ga watan Disamba shekerar 1998 Dr. Emmanuel I. Makoju ya karɓe shugabancin kwalejin wanda ya shugabanci kwalejin har sau biyu shekara 8 kenan bayan saukar shi a (2006). A watan Oktoba shekarar 2006 an naɗa Alhaji Shehi T Sidi a matsayin shugaban kwalejin na wucin gadi har tsawon shekaru 3. Shugaban ƙasa Dr. An sake Dr. Nathaniel O. Odediran a matsayin shugaban kwalejin bayan ya gama zagaye na farko na shugabantar kwalejin, shugaban ƙasa Dr Goodluck Ebele Jonathan ya sake naɗa shi a matsayin shugaban kwalejin har shekara ta 2018.
An naɗa Alhaji Jibril Garba a matsayin shugaban kwalejin na riƙon ƙwarya tsawon watanni 3.
Ranar 10 ga watan Afrilu shekara ta ta 2018 Gwamnatin tarayya ta naɗa Farfesa Faruk Rasheed Haruna a matsayin shugaban kwalejin, wanda har zuwa yanzu magana da ake shine shugaban makarantar.
Kwasa-kwasai da ake koyarwa a kwalejin
Waɗannan sune jerin darussan da ake koyarwa a kwalejin Kontagora
- Adult and Non-Formal Education
Agricultural Science
- Agricultural Science and Education
- Arabic / Christian Religious Studies
- Arabic / English
- Arabic / French
- Arabic / Hausa
- Arabic / Igbo
- Arabic / Islamic Studies
- Arabic / Social Studies
- Arabic / Yoruba
- Biology / Chemistry
- Biology / Integrated Science
- Biology / Mathematics
- Biology / Physics
- Business Education
- Christian Religious Studies / Economics
- Christian Religious Studies / English
- Christian Religious Studies / French
- Christian Religious Studies / Geography
- Christian Religious Studies / History
- Christian Religious Studies / Hausa
- Christians Religion Studies / Social Studies
- Christians Religion Studies / Yoruba
- Computer Science Education / Mathematics
- Early Childhood Care Education
- Economics / English
- Economics / Mathematics
- Economics / Social Studies
- Education and Arabic
- Education and Biology
- Education and Christian Religious Studies
- Education and English Language
- Education and Hausa
- Education and Integrated Science
- Education and Islamic Studies
- Education and Mathematics
- Education and Physics
- Education and Social Studies
- English / French
- English / Hausa
- English / History
- English / Igbo
- English / Integrated Science
- English / Islamic Studies
- English / Political Science
- French / Social Studies
- French / Hausa
- French / History
- French / Igbo
- French / Yoruba
- Geography / Mathematics
- Geography / Social Studies
- Hausa / Igbo
- Hausa / Islamic Studies
- Hausa / Political Science
- History / Islamic Studies
- Igbo / Social Studies
- Igbo / Yoruba
- Integrated Science / Mathematics Education
- Integrated Science / Yoruba
- Islamic Studies / Economics
- Islamic Studies / Geography
- Islamic Studies / Social Studies
- Islamic Studies / Yoruba
- Mathematics / Physics
- Mathematics / Social Studies
- Physical and Health Education
- Political Science / Social Studies
- Primary Education Studies
- Social Studies / Yoruba
- Teacher Education Science
- Physical And Health Education (Double Major)
- Computer Science / Biology
- Computer Science / Chemistry
- Computer Science / Physics
- Fine And Applied Arts (Double Major)
- Special Education (Double Major)
- Social Studies (Double Major)
- Primary Education ( Double Major)
- Home Economics (Double Major)
Manazarta