Mahathir bin Mohamad Kalmar|Jawi: محاضير بن محمد; IPA: IPA-may|maˈhaðɪr bɪn moˈhamad|; An haife shi a ranar 10 ga watan yunin shekara ta 1925)[1] dan siyasar kasar Malasiya ne kuma firayim minista maici ayanzu karo nabiyu. Shine Shugaban gamayyar Pakatan Harapan,[2] kuma danmajalisar kasar, dake wakiltar mazabar tarayya ta Langkawi dake Kedah. Kafin nan yarike firayim minista daga shekarar 1981 zuwa shekara ta 2003, inda yazama wanda yafi dadewa a karagar. Siyasar Mahathir tafi tsawon shekara saba'in (70) tun bayan shigarsa sabuwar jam'iyar United Malays National Organisation (UMNO) a shekarar 1946; ya kirkira jam'iyar Kansa wato Parti Pribumi Bersatu Malaysia (Malaysian United Indigenous Party), a shekara ta 2016.[3][4]
An haife shi da girmarsa a Alor Setar, Kedah, Mahathir yakasance maikwazo a makaranta haka yasa yazama likita. Yazama jigo a cikin jam'iyar UMNO kafin yaje Majalisa a shekarar 1964. Yayi tenuwa daya ne kawai, sai yakasa cin kujerarsa kuma yayi rashin nasara ne da firayim ministan waccan lokaci wato Tunku Abdul Rahman[5] kuma an koreshi daga jam'iyar UMNO. Yayin da Abdul Rahman yayi marabus, Mahathir yasake shiga UMNO da zuwa Majalisa, kuma Karin girma zuwa fadar gwamnati, a sheakarar 1976 yakai matsayin mataimakin firayim minista, kuma a shekarar 1981 aka rantsar dashi a matsayin firayim minista bayan ubangidansa yayi marabus, Hussein Onn.
A lokacin mulkin Mahathir a matsayin firayim minista na farko, kasar Malaysia tasamu cigaban zamani da farfadowar tattalin arziki, kuma gwamnati ta fara kafa ayyukan gine-gine. Mahathir yakasance Shugaban daya jima a mulki, yayi nasara harsau biyar a babban zaben Kasar. A matsayin sa na firayim minista ya rika rajin cigaban kasashen da basu da karfin tattalin arziki da duniya bakidaya.
Bayan yanar mulki, Mahathir yazama mai sukan Shugaban daya zaba da hannunsa yagaje shi Abdullah Ahmad Badawi a shekarar 2006, da kuma Najib Razak a shekara ta 2015.[6] dansa Mukhriz Mahathir shine Chief Minister dake Kedah har zuwa farkon shekara ta 2016. A ranar 29 ga watan February shekarar 2016, Mahathir yafita daga jam'iyar UMNO dalilin goyon bayan firayim minista Najib Razak, dukda 1Malaysia Development Berhad scandal.[7] A 9 September 2016, yayi wa jam'iyar sa Malaysian United Indigenous Party rijista a matsayin jam'iyar siyasa, kuma shine Shugaban ta.[8] A ranar 8 ga watan January 2018, Mahathir yazama Dan takarar jam'iyar gamayyar Pakatan Harapan danyin takarar firayim ministan Malaysia a babban zaben 2018, a wani shirin yafewa Anwar Ibrahim da kuma iya bashi mukami idan ansamu nasara.
Bayan samun nasarar jam'iyar Pakatan Harapan a zaben shekarar 2018, An rantsar da firayim minista Mahathir a ranar 10 ga watan Mayu shekarar 2018. Yana da shekaru 98, shine tsohon Shugaban kasa maici a duniya.[9] shine firayim minista dabai wakiltar YAN jam'iyar gamayyar Barisan Nasional ko wanda tagabace ta Alliance Party kuma mutum na farko da yayi mulki Katsina jam'iya biyu daban daban kuma ba'a Jere ba.
↑"Dr Mahathir's new party officially registered". Free Malaysia Today FMT News. 9 September 2016. Archived from the original on 15 October 2016. Retrieved 15 October 2016. More than one of |archiveurl= and |archive-url= specified (help); More than one of |archivedate= and |archive-date= specified (help)