Lawal Kaita (An haife shi ne a ranar 4 ga Watan Oktoban shekarar 1932) na Miladiyya (A.C) Ya kuma mutu ne a ranar 2 ga watan Janairun shekarar 2018). Ya kasan ce ɗan siyasan Najeriya ne da aka zaba a jam'iyyar National Party of Nigeria (NPN) a matsayin gwamnan jihar Kaduna, Najeriya, ya rike mukami tsakanin Oktoba zuwa Disamban 1983, lokacin Jamhuriyya ta biyu ta Najeriya wacce ta kare da juyin mulkin da ya kawo Janar Muhammadu Buhari kan mulki.[1][2][3]
Haihuwa
An haifi Lawal Kaita a ranar 4 ga Oktoban shekarar 1932 a Katsina, Arewacin Najeriya.[4] Shi ɗan uwan Shugaba Umaru Musa Yar'Adua ne na jini kuma dan gidan sarautar Nagogo, sarakunan gargajiya na masarautar Katsina. Ya halarci Kwalejin Barewa, Zariya (1946 - 19550) sannan daga baya ya yi karatu a Makarantar Tattalin Arziki ta London (1971–1972).. Bayan dawowarsa Najeriya, Kaita ya zama ma'aikacin gwamnatin jihar Kaduna. Ya yi aiki a matsayin Sakatare a Hukumar Ruwa ta Jiha (1973–1975), Kwamishinan Tsare-Tsaren Tattalin Arziki (1975 - 1977) da Mataimakin Babban Sakatare na Ma’aikatar Ayyuka na Jihar Kaduna (1976–1977).[5][6][7]