Kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya Bida makarantar kwaleji ce da ke cikin Jihar Neja, a arewa ta tsakiyar Najeriya . An buɗe ta a cikin shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in da bakwai 1977.
Tarihi
Kwalejin tarayya ta Bida an kafa ta ne a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in da bakwai 1977 biyo bayan shawarar da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yanke na matsar da cibiyar zuwa Bida, Kafin wannan lokacin ana kiranta (kwalejin Fasaha ta Tarayya ce, Kano) .[ana buƙatar hujja]
An fara zaman farko na karatun ne a watan Afrilu, shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in da takwas 1978 tare da ɗalibai ɗari biyu da goma sha ɗaya 211 da manyan ma'aikata guda goma sha ɗaya 11, ƙananan ma'aikata guda talatin da uku 33.Kwalejin kimiyya da fasaha ta Bida babbar makarantar gwamnatin tarayya ce da ke Bida, jihar Neja, Najeriya, a halin yanzu akwai fannoni bakwai a cikin makarantar, [1]