Kabiru Bala, (An haife shi ranar 7 ga watan Junairu a shikara na 1964) farfesa ne, malamin ilimin gine-gine, kuma mataimakin shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a yanzu.[ana buƙatar hujja]
Tarihi
Kabiru ya yi karatu a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya samu digiri na farko a fannin gine-gine da kere-kere a shekarar ta 1985. Ya yi digirinsa na biyu da na uku duk dai a jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya. Yayi wallafe-wallafe sama da 80.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Manazarta