Jami'ar Al-Azhar[1]jami'a ce kuma masallaci ne a Alkahira, Misira. Shi ne babban cibiyar na Adabin Larabci da kuma wajen koyon Ilimin Musulunci a duniya. Hakanan ita ce babbar jami'a ta biyu mafi girma a duniya. [2] Mabiya Fatimiyya na al'adun Shi'a ne suka kafa ta a shekara ta 975.