Jaipur birni ne, da ke a jihar Rajasthan, a ƙasar Indiya. Shi ne babban birnin jihar Rajasthan. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar alif dubu biyu da goma sha ɗaya 2011, akwai jimilar mutane miliyan ukku da dubu arba'in da shida da ɗari da sittin da uku 3,046,163. An gina birnin Jaipur a karni na sha takwas bayan haifuwan annabi Issa.