Josiah Onyebuchi Johnson Okezie (1923-2002) likita ne kuma ɗan siyasa ɗan Najeriya wanda ya kasance ministan lafiya kuma daga baya ya zama minister noma a gwamnatin Yakubu Gowon.[1]
A jamhuriya ta farko, Okezie ya jagoranci jam'iyyar Republican, jam'iyyar da ba ta da rinjaye ta kulla kawance da NPC da NNDP karkashin jagorancin Akintola.[2] A cikin shekarar 1970s, ƙoƙarinsa na Ministan Lafiya ya taimaka wajen canza tashar binciken aikin gona a Umudike zuwa cibiyar bincike ta tarayya.[3]
Okezie dan majalisar wakilai ne daga baya ya koma NPN a jamhuriya ta biyu. Sunansa ya fito cikin wadanda ake ganin a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar, Shehu Shagari.[4]
Ya yi digiri na biyu a Kwalejin Gwamnati da ke Umuahia. Ya kafa Babban Asibitin Ibeku, Umuahia, wanda a bude yake amma abin ya yi kamari a lokacin yakin Biafra.