UseYakubu Gowon, (an haife shi ne a ranar 19 ga watan Oktoban shekarar alif dubu daya da Dari Tara da talatin da uku 1934) a Lur ta jihar Filato, Najeriya.[1] Ana yi masa laƙabi da Jack Gowon, tsohon soja ne kuma shugaban kasarNijeriya. Yakubu Gowon shugaban ƙasar Najeriya ne daga watan Agusta a shekarar alif dubu daya da Dari Tara da sittin da shida 1966, zuwa watan yuli shekarar alif dubu daya da dari tara da saba'in da biyar 1975. (bayan Johnson Aguiyi-Ironsi - kafin Murtala Mohammed). A ƙarƙashin mulkin Gowon ne masu fafutukar neman ficewa daga Najeriya daga al'umman ibo ƙarkashin jagorancin shugaban su Odemegwu Ojukwu don ƙasar Biafara suka janyo yakin basasa tsakanin gwamnatin Najeriya da kuma mutanen Biyafara,[2] inda gwamnatin Gowon ɗin tafito ta yaƙesu har sai da suka miƙa wuya. An kuma ayyana wannan yakin a matsayin daya daga cikin yaki mafi muni a tarihin zamani, yayinda wasu ke zargin Gowon da aikata ta'addanci ga 'yan Adam. Gowon ya bayyana cewa shi bai aikata wani aikin ta'addancci ba, asali ma shugabncin ya kwato kasar ne daga rushewa.[3]
Yakubu Gowon ya kasance mabiyin addinin kiristanci[4] mai akidar anglican daga Kabilar Ngas na arewacin Najeriya,Gowon ya kasance mai kishin kasa,[5] kuma wanda yayi imani da hadin kai da kuma zaman 'yan Najeriya a matsayin tsintsiya guda.[6]
Shine shugaban ƙasan na mulkin soja da ya fi kowa daɗewa akan karagar shugabancin Najeriya, har tsawon shekaru tara.
Sannan kuma wasu sun zargi gowon da kashe adadin mutane masu yawa a dalilin yaƙin Biafra.[7]